Masu Neman Kujerun APC Sun Tada rikici, Sun bukaci Jam’iyya ta Biya su Kudinsu

Masu Neman Kujerun APC Sun Tada rikici, Sun bukaci Jam’iyya ta Biya su Kudinsu

  • Wadanda suka yi takara a zaben jam’iyyar APC sun dade su na jiran a dawo masu da kudin fam
  • Akwai mutum 126 da suka nemi kujeru a majalisar NWC, amma jam’iyyar ta ki bari a shiga zabe
  • Ganin an fitar da shugabanni ta hanyar maslaha, aka bukaci a dawowa ‘yan takaran kudinsu

Abuja - Punch tace Ran ‘ya ‘yan jam’iyyar APC da suka nemi kujerun NWC ya baci bayan hana su mukaman da aka yi, kuma aka rike masu kudinsu.

Wadanda suka shiga zaben shugabannin jam’iyyar APC na kasa a watan Maris sun hakura bayan da aka tsaida duka shugabannin ta hanyar maslaha.

Tun a lokacin ake cewa za a dawowa wadannan mutane da kudinsu, ganin cewa ba a bada damar an kada kuri’a wajen tsaida sababbin shugabannin ba.

Kara karanta wannan

Kaico: Dan takarar shugaban kasa ya soki su Buhari saboda gaza gyara wutar lantarki

The Nation tace abin ya kai wasu sun fara barazanar kai shugabannin jam’iyyar kotu ganin cewa an shafe tsawon watanni hudu, kudinsu ba su dawo ba.

Su wanene suka janye takara

Wadanda suka nemi mukamai a majalisar ta NWC sun biya N2m zuwa N20.5m domin sayen fam, a karshe aka bukaci sama da mutum 125 su janye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar APC ta nemi Tanko Al-Makura, Salihu Mustapha, Sani Musa, Abdulaziz Yari, George Akume da Mohammed Etsu su janyewa Abdullahi Adamu.

Shugaban APC
Shugaban APC, Abdullahi Adamu Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

A bangaren mataimakan shugaban jam’iyya akwai su, Yakubu Dogara, Faruq Aliyu, Sylvester Monidefe, Ken Nnamani, Isa Yuguda da Emmanuel Joseph.

Adebayo Shittu, Oyedele Ifeoluwa da Olaiya Olaitan sun hakura da neman kujerar Sakatare bayan sun biya fam, aka zabi Iyiola Omisore daga jihar Osun.

Daga cikin mutane 126 da suka janye takararsu akwai Yekini Nabena da Worgu Chambers.

Kara karanta wannan

Bayan Wata 4 rak a Ofis, An Soma Yunkurin Raba Adamu da Shugabancin APC

“Lafin Sanata Abdullahi Adamu ne”

A hira dabam-dabam da aka yi da ‘ya ‘yan jam’iyyar mai mulki, sun zargi shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu da kawo cikas wajen dawo da kudin.

Jam’iyya ta tara fiye da N700 daga kudin fam a lokacin zaben shugabanni na kasa, duk da haka jaridar Sun tace ana kukan ba a kula da ma’aikatan APC.

Uwar jam'iyya ta bada hakuri

Mai magana da yawun bakin APC na kasa, Felix Morka ya shaidawa manema labarai cewa uwar jam’iyya tana aiki a kan wannan batu na kudin sayen fam.

Shi ma mataimakin shugaban APC, Salihu Lukman ya koka game da lamarin, ya nuna cewa ya kamata a ce an maidawa ‘yan takaran kudinsu tun tuni.

ADC ta shiya takara a Kano

A makon nan aka ji labari cewa Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada mai wakitar Karamar Hukumar Birni a Jihar Kano ya shiga jam’iyyar hamayya ta ADP.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa ba za ta yiwu a tunbuke Shugaban kasa ba inji Tsohon Sanatan PDP

Hon. Sharada zai yi takarar kujerar gwamnan Kano a karkashin ADP bayan shan kashi jam’iyyar APC wajen neman tikitin zama 'dan takarar Gwamna a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng