Bangaren Shekarau Ta Magantu Kan Jita-Jitar Komawarsa PDP

Bangaren Shekarau Ta Magantu Kan Jita-Jitar Komawarsa PDP

  • Sanata Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan Jihar Kano ya musanta rahoton cewa yana shirin fita daga jam'iyyar NNPP ya koma PDP
  • Sanatan mai wakiltar Kano Central ya bayyana hakan ne ta bakin hadiminsa Malam Bello Sharada amma ya tabbatar Atiku ya yi wa Shekarau tayi sai dai kwamitin Shura ba ta amince ba
  • Bello Sharada ya kuma bayyana cewa wasu daga bangaren Malam Shekarau sun yi korafin cewa Sanata Rabiu Kwankwaso bai cika musu alkawarin da ya yi na basu tikiti ba a NNPP

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya yi watsi da tayin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar na komawa PDP.

Hadimin Sanata Shekarau, Malam Bello Sharada, ya fada wa Sahelian Times a ranar Talata, ya kara da cewa kwamitin Shura ta Ibrahim Shekarau ta yi amincewa da neman da PDP ke yi na sanatan da ke wakiltan Kano Central ya koma PDP.

Kara karanta wannan

Shekarau Zai Fita Daga NNPP Ta Kwankwaso Ya Koma PDP Saboda Wasu Alƙawurra 'Masu Tsoka' Da Atiku Ya Masa

Shekarau da Kwankwaso
Bangaren Shekarau Ta Magantu Kan Jita-Jitar Komawarsa PDP. Hoto: @saheliantimes.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sharada ya kara da cewa a yayin taron da aka yi a ranar Lahadi, 14 ga watan Agusta na 2022 a gidan Shekarau na Mundubawa a Kano, an tattauna wasu muhimman abubuwa baya da tayin da Atiku Abubakar ya yi.

"Ka san cewa Malam Shekarau ya taba takarar shugaban kasa a tsohuwar jam'iyyar ANPP, hakan yasa wasu yan takarar shugaban kasa ke tuntubarsa. Kuma a wurin irin wannan tarukan ne suka hadu da Atiku kuma ya masa tayin ya koma PDP."

Ya bayyana cewa lokacin da kwamitin shura suka zauna taro a ranar Lahadi, sun tattauna ganawar Shekarau da Atiku sanna suka yanke shawarar Shekarau ba zai karbi 'tayin da ya masa mai gwabi ba'.

Sharada ya tabbatar da cewa wasu a bangaren Shekarau sunyi korafi

Hadimin na Shekarau ya tabbatar da cewa wasu a bangaren tsohon gwamnan na Kano sun koka kan abin da suke yi wa kallon rashin adalci da saba alkawari da Kwankwaso ya yi, rahoton Sahelian Times.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Yadda Gwamna El-Rufai Yake Taimakawa Wajen Jawo Matsalar Tsaro

Ya tunatar cewa yayin tattaunawa da aka yi kafin sanatan ya koma NNPP, an masa alkawarin tikitinsa da na wasu magoya bayansa ba tare da hamayya ba, amma Kwankwaso bai cika alkawarin ba kawo yanzu don kawai Shekarau shi kadai ya samu tikitin.

"Ka ga, ba mu da yan takarar majalisar wakilai na tarayya, da na majalisar dokokin jiha a zaben 2023. Ba mu da wakilai a shugabancin jam'iyya, tikitin Malam Shekarau kadai Kwankwaso ya cika alkawarin hakan."

A baya, wata jaridar kafar intanet ta rahoto cewa Shekarau ya yi mabanbanta taruka da Atiku Abubakar, da abokin takararsa Ifeanyi Okowa da shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, kan jita-jitar komawarsa PDP.

Shekarau Zai Fita Daga NNPP Ta Kwankwaso Ya Koma PDP Saboda Wasu Alƙawurra 'Masu Tsoka' Da Atiku Ya Masa

Tunda farko, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau zai sanar da ficewarsa daga NNPP zuwa PDP biyo bayan wani alƙawari 'mai tsoka' da aka ce dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar ya masa.

Mista Shekarau, wanda ke wakiltar Kano Central, ya sanar da ficewarsa a hukumance daga APC zuwa NNPP cikin wata wasika da shugaban majalisa, Lawan Ahmad ya karanto a ranar 29 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel