Peter Obi Na Neman ba Atiku Ciwon-kai, Ya yi Kus-kus da Manyan PDP cikin dare
- Mai neman kujerar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi ya kai ziyara zuwa garin Fatakwal
- Peter Obi ya yi zama na musamman da Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da wasu mutanensa
- Sauran wadanda aka yi zaman da su sun kunshi tsofaffin Gwamnoni da Gwamnoni masu-ci
Rivers - ‘Dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar hamayya ta Labour Party watau Peter Obi, ya sake haduwa da Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
Punch ta fitar da rahoto dazu cewa Peter Obi ya gana da su Gwamna Nyesom Wike a ranar Litinin. An yi zaman ne yayin da PDP ke fama da rikicin gida.
Wannan karo jagororin jam’iyyar PDP da-dama su na cikin wadanda aka yi zaman da su. Zuwa yanzu ba mu da masaniya kan abin da aka tattauna a taron.
Baya ga Wike, Obi ya zauna da tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko wanda ya yi mulki har na tsawon shekaru takwas a karkashin jam’iyyar ZLP.
Su wanene suka halarci zaman?
Daily Post tace wadanda aka sa labule da su a daren na yau sun kunshi; tsohon gwamnan jihar Kuros Riba, Donald Duke, sai Ibrahim Dankwambo.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Dankwambo wanda ya yi gwamna a Gombe tsakanin 2011 da 2019 yana cikin na hannun daman Wike, ya mara masa baya zaben tsaida 'dan takara.
Rahoton yace sauran wadanda suka halarci wannan zama su ne Gwamnoni masu-ci na jihohin Abia da Benuwai; Vivtor Okezie Ikpeazu da Samuel Ortom.
Wani wanda ya halarci wannan zama a Fatakwal shi ne tsohon Ministan shari’a a gwamnatin Goodluck Jonathan watau Mohammed Bello Adoke SAN.
An yi wannan taron ne a gidan Mai girma Wike da yake garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas. Maza akalla 10 da mace daya suka yi wannan zama.
Mun fahimci Segun Mimiko ya daura hotunan haduwar ‘yan siyasan a shafinsa na Twitter, inda aka ji yana cewa ya yi farin cikin haduwa da mutanen.
“Na ji dadin kashe lokaci a daren jiya tare da @GovWike, @Donald_Duke, @PeterObi, @HEDankwambo, @GovSamuelOrtom, @GovernorIkpeazu, da Mohammed Adoke SAN da wasu tulin abokai.”
- Segun Mimiko
Wannan ne karo na biyu da aka ga Peter Obi tare da Wike a fili tun bayan zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP, wanda Atiku Abubakar ya yi galaba.
Wike ya fallasa 'Yan PDP
An ji labari Nyesom Wike ya fasa-kwan jagororin PDP, ya tona wadanda suka hana a ba shi tikitin Mataimakin Shugaban kasa a zaben Najeriya na 2023
Wike ya ci burin Atiku Abubakar zai dauke shi a matsayin abokin takararsa, bayan ya rasa tikitin Jam’iyyar, amma aka dauko Gwamna Ifenayi Okowa.
Asali: Legit.ng