2023: Kwadayi Ya Jawo APC Ba ta da ‘Yan Takaran Sanata a Yobe da Akwa Ibom

2023: Kwadayi Ya Jawo APC Ba ta da ‘Yan Takaran Sanata a Yobe da Akwa Ibom

  • Hukumar zabe na INEC ba ta amince da takarar Ahmad Lawan da Godswill Akpabio a 2023 ba
  • Jam’iyyar ta bada sunayen Lawan da Akpabio, amma INEC tace ba da suka ayi neman tikiti ba
  • APC ta rasa shiga takarar Sanata a Arewa maso yammacin Akwa Ibom da Arewacin jihar Yobe

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Hukumar zabe na kasa watau INEC ta ki karbar Ahmad Ibrahim Lawan da Godswill Akpabio a matsayin ‘yan takarar kujerar Sanata a 2023.

PM News ta rahoto Kwamishinan INEC, Festus Okoye yana cewa hukumar zabe ba ta san da zaman Ahmad Ibrahim Lawan da Godswill Akpabio ba.

Dr. Ahmad Lawan da Godswill Akpabio su na neman kujerar majalisar dattawa na mazabun Arewacin Yobe da Arewa maso yammacin Akwa Ibom.

Rahoton yace takarar manyan ‘yan siyasan sun gamu da cikas bayan da hukumar zabe mai zaman kanta tace jam’iyyar APC ba ta da ‘yan takara.

Kara karanta wannan

An Kafa Kwamitin Mutum 14 da Zai Kawo Karshen Rikicin Atiku da Wike a PDP

Tun 2007, Lawan yake Sanatan Yobe ta Arewa, a 2019 ya zama shugaban majalisa. Akpabio ya rike kujerar Sanatan Akwa Ibom daga 2015 zuwa 2019.

Okoye yace APC sun gabatar da sunayen wadannan mutane a matsayin ‘yan takaran, amma sun fahimci ba su ne suka lashe zaben tsaida gwani ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lawan
Shugaban majalisar dattawa ya je takarar shugaban kasa Hoto: @NgrSenate
Asali: Facebook

Kwamishinan ya yi wannan karin-haske ne a lokacin da aka yi hira da shi a tashar Channels TV. Wannan ya kawo karshen gardamar da ake yi kan tikiti.

“A wadannan mazabu biyu, an kawo sunaye biyu, hukumar ta gano sunayen ba na wadanda suka shiga zaben tsaida gwani da jam’iyyun suka shirya ba ne.
Saboda haka ba mu wallafa sunayensu ba. Halin da muke ciki kenan a halin yanzu."
“APC ta daura sunayen (Lawan da Akpabio) a shafin mu, amma binciken mu ya nuna ba su ne ‘yan takaran da suka yi nasara a zaben fitar da gwani ba.”

Kara karanta wannan

Yarda Zai Yi Wa Tinubu Aiki ya Jefa Gwamna a Matsala, Ana yi wa Addininsa Barazana

“Hukumar ba ta daura sunayensu da bayanansu a mazabunsu ba. Saboda haka, maganar da ake yi shi ne APC ba ta da ‘yan takara a mazabun nan.”

- Festus Okoye

Za a sauke Abullahi Adamu?

Abullahi Adamu ya zama Shugaban APC na kasa ne a watan Maris, bayan ya ajiye kujerar Sanata sai ga shi labari ya zo cewa wasu na neman a tunbuke shi.

Ana zargin Shugaban na APC da sakaci da zaben 2023, kuma ana ganin ya kamata Kirista ya rike kujerar tun da Musulmai aka ba takarar shugabancin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng