Wike Ya Yi Magana Kan Karar Da Aka Shigar Na Neman Tsige Atiku A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa

Wike Ya Yi Magana Kan Karar Da Aka Shigar Na Neman Tsige Atiku A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa

  • Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, ya ce bai shigar da kara a kotu na neman tsige Atiku ba a matsayin dan takarar shugaban kasa na PDP
  • An rahoto cewa an shigar da karar ne da sunan Wike da wani jigo na jam'iyyar PDP aka nemi kotu ta cire sunan Atiku daga jerin sunayen yan takarar shugaban kasa na 2023
  • Amma, Gwamna Wike, ya musanta cewa shine ya shigar da karar ya bayyana shi a matsayin aikin masu neman tada rikici

Nyesom Wike, gwamnan Jihar Rivers ya nesanta kansa daga ƙarar da aka rahoto cewa an shigar a kotu na neman soke Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, kamar yadda ThisDay ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yarda Zai Yi Wa Tinubu Aiki ya Jefa Gwamna a Matsala, Ana yi wa Addininsa Barazana

Magoya bayan Wike sun kai Atiku da Aminu Tambuwal, gwamnan Jihar Sokoto da hukumar INEC kotu kan yadda aka yi zaben fidda gwani na shugaban kasa na PDP da aka yi a watan Mayu.

Gwamna Wike
Wike Ya Yi Magana Kan Karar Da Aka Shigar Na Neman Tsige Atiku A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa. Photo credit: Gov Nyesom Ezenwo Wike - CON
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ƙarar da aka shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/782/2022, Newgent Ekamon da wasu masu shigar da karar sun bukaci kotun tarayya ta Abuja ta umurci INEC ta cire Atiku daga jerin sunayen yan takarar shugaban kasa na zaben 2023.

Masu shigar da karar sun bukaci kotu ta umurci PDP da ayyana Wike a matsayin dan takarar shugaban kasa kuma wanda ya lashe zaben fidda gwani na ranar 28 da 29 na Mayun kuma ta umurci PDP ta mika sunansa a matsayin dan takarar zaben shugaban kasa, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike ya Kai Atiku da Tambuwal Kotu, yace Shi ne Asalin ‘Dan takaran PDP

Wike ya sha kaye ne hannun Atiku bayan Tambuwal ya janye wa tsohon mataimakin shugaban kasar ya umurci magoya bayansa su zabe shi.

Yayin da tsohon mataimakin shugaban kasar ya samu kuri'u 371 da ya bashi damar zaman ɗan takarar PDP, Wike ya samu kuri'u 237 ya zo na biyu.

Sakamakon zaben ya janyo rabuwar kai a jam'iyyar ta PDP.

Abin da Wike ya ce game da karar da aka shigar kan Atiku da PDP

Da ya ke magana a hirar da ThisDay ta yi da shi a ranar Juma'a, Wike ya ce bai umurci wani ya shigar da kara a madadin sa ba

"Ban san komai game da karar ba. Ban ce wani ya shigar min da kara ba," aka rahoto gwamnan yana cewa.

"Ban san lauyoyin ba. Shin ni karamin yaro bane da zan shigar da kara yanzu? Ina da kwana 14 bayan zaben fidda gwanin idan ina son shigar da kara. Ban yi hakan ba a lokacin, sai wata biyu bayan zaben fidda gwani zan shigar da kara?

Kara karanta wannan

‘Yan Takara Sun Dauko ta da zafi, Sun yi wa Atiku Abubakar alkawarin Kuri’u Miliyan 20

"Jiya ma sun kirkiri wani batun wai na umurci babban jami'in tsaro na ya saukar da tutan PDP a gidan gwamnati. Wannan karya ne, duk farfaganda ne. Wasu na kokarin amfani da ni su ci zabe. Don Allah ku yi watsi da karerayin nan."

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164