Laifin Tinubu Ne "Idan Amaechi Ya Koma PDP", Babban Jigon APC Ya Fasa Kwai
- Wani na hannun daman Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri, Chukwuemeka Eze, ya ce akwai yiwuwar tsohon gwaman Jihar Rivers din zai koma PDP
- Eze, ya yi ikirarin cewa laifin dan takarar shugaban kasa na APCn, Bola Ahmed Tinubu ne da shugabannin jam'iyyar suka yi sanadin barinsa jam'iyyar
- Na hannun daman na Amaechi yana magana ne a kan zargin cewa dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar na zawarcin tsohon ministan
Port Harcourt, Rivers - Chukwuemeka Eze, fitaccen jagora a jam'iyyar APC kuma na hannun daman Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri, ya ce a dora wa Bola Tinubu laifi idan Amaechi ya bar jam'iyyar.
Eze yana magana ne kan wani rahoto da ke ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar yana zawarcin Amaechi, The Punch ta rahoto.
2023: Babangida Aliyu Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Atiku Zai Ci Jihar Rivers Da Sauran Jihohin Kudu Maso Kudu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da yasa Amaechi zai iya shiga PDP - Na hannun damansa ya bayyana
Idan za a iya tunawa Eze a baya-bayan nan ya kasance yana magana kan Amaechi kuma ya ce idan Amaechi ya shiga PDP, laifin Tinubu ne, wato dan takarar shugaban kasa na APC.
Ya yi ikirarin cewa a dora wa tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar mai mulki idan tsohon ministan ya fita daga APC.
"Idan Amaechi ya yanke shawarar shiga PDP, ta yi wu ba laifinsa bane amma saboda abubuwa da halin Sanata Bola Ahmed Tinubu da masu kula da kamfen dinsa tare da sabbin shugabannin da ke tafiyar da harkokin APC a yanzu," in ji Eze.
2023: Babangida Aliyu Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Atiku Zai Ci Jihar Rivers Da Sauran Jihohin Kudu Maso Kudu
Tinubu na kawai karfe 4 na dare bai yi barci ba yana aiki saboda tsananin kwazonsa , Shugaban matasan APC Dayo Isarel
A wani rahoton, tsohon gwamnan Jihar Neja, Dakta Babangida Aliyu Mua'zu ya ce yana kyautata zaton dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar zai ci jihar Rivers a babban zaben 2023, Leadership ta rahoto.
Ya ce Rivers ta gaba daya kudu maso kudu yanki ne na PDP bisa la'akari da tarihi don haka ya bukaci masu ruwa da tsaki su tabbatar an maimaita nasarorin da aka saba samu a zabukan shugaban kasa na baya.
Asali: Legit.ng