2023: Babangida Aliyu Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Atiku Zai Ci Jihar Rivers Da Sauran Jihohin Kudu Maso Kudu

2023: Babangida Aliyu Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Atiku Zai Ci Jihar Rivers Da Sauran Jihohin Kudu Maso Kudu

  • Dakta Babangida Aliyu, tsohon gwamnan Jihar Neja ya ce Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP zai ci jihar Rivers
  • Jigon na jam'iyyar PDP ya ce idan aka yi la'akari da tarihi dama PDP ta saba cin zaben shugaban kasa a Rivers da sauran jihohin kudu maso kudu
  • Ya ce rikicin siyasa tsakanin Atiku da Wike ba zai hana PDP ta ci jihar ba duk da cewa suna kokarin yin sulhu na gaskiya kuma wanda zai kawo amfani ga jam'iyyar baki daya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT Abuja - Tsohon gwamnan Jihar Neja, Dakta Babangida Aliyu Mua'zu ya ce yana kyautata zaton dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar zai ci jihar Rivers a babban zaben 2023, Leadership ta rahoto.

Atiku
2023: Atiku Zai Kawo Jihar Rivers Da Kudu Maso Kudu, In Ji Babangida Aliyu. Hoto: @LeadershipNGA.
Asali: Twitter

Ya ce Rivers ta gaba daya kudu maso kudu yanki ne na PDP bisa la'akari da tarihi don haka ya bukaci masu ruwa da tsaki su tabbatar an maimaita nasarorin da aka saba samu a zabukan shugaban kasa na baya.

Kara karanta wannan

Ta karewa PDP a Sokoto yayin da fitaccen kwamishina ya kaura, ya koma APC

Blueprint ta rahoto cewa Babangida ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da kwamitin tsare-tsare na PDP na Ward 2 da za su hallarci taro na kasa da za a gudunar a farkon wata mai zuwa.

Ya ce kada a tada hankali kan rikicin siyasa da ke tsakanin dan takarar shugaban kasa Atiku da gwamnan jihar Nyesom Wike, amma jam'iyyar ta kafu a jihar don haka ba za ta fadi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban sashin watsa labarai na kwamitin tsare-tsare, Dr Golu Timothy, ya ambato Babangida na cewa kada yan jam'iyyar su ji tsoro ko kuma kada su damu da abin da ke faruwa, amma su sa rai cewa za su yi nasara a babban zaben da ke tafe.

Ya kara da cewa jam'iyyar tana da ra'ayin yin sulhu amma sulhu da zai kawo sakamako.

Za mu saka ido kan wadanda muka bawa kudi gabanin zabe, Aliyu

Kara karanta wannan

A Karshe, Buhari Ya Yi Magana Kan Abin Da Ya Janyo Yakin Basasa Na 1967, Ya Bayyana Mafita Ga Najeriya

Jigon na PDP ya ce wannan karon za a yi takatsantsan don ganin cewa duk wani kudi da aka bada an yi amfani da shi don abin da ya dace.

"Nagode bisa aikin da W2W ke yi. Ku ne ke kusa da mutane kuma muna alfahari da ku. Dalilin kamfen din shine don Atiku ya yi nasara, amma akwai aiki a gaban mu don cimma hakan. Ku yi amfani da kudin ta don dalilin da aka bada. Kasar nan na bukatar Atiku. Ku koma mazabar ku ku basu sakon fata na gari, kada mu tsaya a Abuja muna turanci."

Atiku: Tikitin Musulmi Da Musulmi Yasa Ban Amince Da Tinubu Ba Lokacin Da Yake Son Zama Abokin Takara Na

A wani rahoton, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce kauracewa tikitin musulmi da musulmi yasa ya ki yarda Asiwaju Bola Tinubu ya yi masa mataimaki a zaben shekarar 2007, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku da Wike: Jam'iyyar PDP ta dage zaman NEC saboda ta'azzarar rikicin gida

Atiku, wanda ya yi wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo mataki daga 1999 zuwa 2007, ne ya bayyana haka yayin wata hira da aka yi da shi a ARISE TV a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel