Bayan Shan Kaye A Zaben Fidda Gwani, Dan Uwan Shugaba Buhari Ya Fice Daga APC

Bayan Shan Kaye A Zaben Fidda Gwani, Dan Uwan Shugaba Buhari Ya Fice Daga APC

  • Ɗan uwan shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, watau Fatuhu Muhammadu, ya fice daga jam'iyyar APC
  • Honorabul Fatuhu ya kasance ɗan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Daura, Mai'Adua da Sandamu a majalisar wakilai
  • Duk da bai bayyana dalilinsa ba, amma ana ganin ya ɗauki matakin barin APC ne bayan rasa tikitin zarcewa kan kujerarsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaatsina - Ɗan uwan shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, watau Honorabul Fatuhu Muhammadu, ya fice daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Honorabul Fatihu, Ɗan babbar yayar shugaban ƙasa Buhari, shi ne mai wakiltar mazaɓar Daura/Mai’Adua/Sandamu a majalisar dokokin tarayya.

Dan uwan shugaba Buhari.
Bayan Shan Kaye A Zaben Fidda Gwani, Dan Uwan Shugaba Buhari Ya Fice Daga APC Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Ya gaza samun tikitin takarar zarcewa kan kujerarsa a zaɓen fidda gwanin APC da ya guda watannin baya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Fatuhu ya samu kuri'u 30 yayin da babban abokin hamayyarsa kuma wanda ya kwaɗa shi da ƙasa, Aminu Jamo, ya samu kuri'u 117, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Sunayen Jihohi 20 da Jam'iyyar APC Ka Iya Shan Kaye a Zaɓe Saboda Rikici

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wasikar murabus daga APC

A wata Wasika da ya aike wa shugaban APC na gundumar Sarakin Yera A, Fatuhu, ya gode wa jam'iyyar bisa ba shi damar zama a inuwarta.

Ya ce:

"Ina mai sanar da kai cewa na yi murabus daga kasancewa mamban APC nan take kuma matakin zai soma aiki ne daga ranar 13 ga watan Yuli, 2022. Haɗe da takardar ga katin rijistar zama mamban jam'iyyata nan KT/DRA/10/00002."
"Yayin da nake miƙa godiyata ga jam'iyya bisa damar da ta bani na wakiltar mutanen mazaɓar Daura/Mai’Adua/Sandamu lokacin da nake cikin jam'iyya, ina son ku karbi fatan Alheri na dan Allah."

Duk da wasikar na ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Yuli amma hadimin ɗan majalisar, Ahmed Ganga, ya saketa a kafafen sada zumunta ne kusan wata ɗaya bayan rubutata.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: Jami'an NDLEA Sun Kama Wani Soja Mai Ritaya Ɗan Shekara 90 Dake Kaiwa Yan Bindiga Kwayoyi

A wani labarin kuma Wata Sabuwa A Rikicin PDP, Gwamna Wike Da Atiku Abubakar Sun Cimma Wata Matsaya Ɗaya

Ga dukkan alamu jam'iyyar PDP ta fara nemo bakin zaren game da rikicin ɗan takararta, Atiku Abubakar da gwamna Wike.

Wani ƙusa a jam'iyyar ya tabbatar da cewa ganawar mutanen biyu ta yi armashi har sun fara lalubo hanyar sasantawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel