2023: Ko ba Wike Zan iya Nasara a Zaben 2023, Atiku ya shaidawa Dattawan PDP

2023: Ko ba Wike Zan iya Nasara a Zaben 2023, Atiku ya shaidawa Dattawan PDP

  • Kurar da ta bade jam'iyyar PDP a zaben fidda gwani na shugaban kasa da ya gudana har yanzu ba ta lafa ba
  • Zaben gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kawo cikas ga jam'iyyar
  • A ganawar da Atiku ya yi Gwamna Nyesom Wike, an ce ba ta kai ga cimma nasarar sulhu ba, domin bangarorin biyu sun gaza samun matsaya guda

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Rahoton jaridar The Nation ya nuna cewa ganawar da Atiku Abubakar ya yi da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ta gaza kawo wani sauyi a rikicin da ke tsakaninsu.

A cewar rahoton, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya gana da gwamnan a gaban kwamitin amintattu na jam’iyyar (BoT), karkashin jagorancin Sanata Walid Jibrin.

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Samu Babban Tawaya A Yayinda Fitaccen Jigonta Ya Yi Murabus Daga Jam'iyyar

Atiku ya bayyana kwarin gwiwar cin zabe ba tare da Wike ba
2023: Zan iya nasara ba tare da Wike ba, Atiku ya shaidawa mambobin Bot na PDP | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

An ce tsohon ministan yada labarai da al’adu, Farfesa Jerry Gana ne ya shirya taron a gidansa.

A wani taro da mambobin BoT na PDP a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta, Atiku ya bayyana cewa PDP za ta iya lashe zaben badi ba tare da kuri’un jihar Ribas ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce babu wani abin fargaba idan Wike bai so ya goyi bayansa ba a yakin neman zabensa.

Cike da kwarin gwiwa, Atiku ya tuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda shi ma bai ci jihar Ribas ba, ya dogara ne da kuri’u daga jihohin Legas, Kano da sauran jihohin da ya kamata ya lashe zaben shugaban kasa na 2019.

Ya kuma ce PDP ta shiga taskun rikici ne saboda Wike ya sanya batun kudi a zaben fidda gwani na shugaban kasa da aka gudanar.

Kara karanta wannan

Kuri'ar Gamsuwa: PDP Ta Aminta Da Salon Jagorancin Ayu Duk Da Rikicin Jam'iyyar

Mutanen Wike na neman a sake fasalin PDP

A halin da ake ciki, masu biyayya ga Wike sun yi kira da a sake fasalin shugabancin PDP don kara samun karbuwa a kudu, suna masu cewa jam'iyyar, kamar yadda take a yanzu, ta fi karfi a Arewa.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, sansanin gwamnan ya koka da yadda tsarin jam’iyyar ya karkata zuwa ga ‘yan Arewa, inda ya jaddada cewa duk wani shirin sulhu tsakanin Atiku da Wike dole ne ya tattauna mafita ga hakan.

Rikicin siyasa: Bayan tsige shi, magoya bayan mataimakin gwamnan PDP sun koma APC

A wani labarin, magoya bayan Rauf Olaniyan da aka tsige daga matsayin mataimakin gwamnan jihar Oyo, sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC a karamar hukumar Iseyin, kamar yadda Daily Independent ta ruwaito.

Hakan ya faru ne a daidai lokacin da ‘yan kungiyar Unity Forum na APC suka bayyana cewa sun yi Makinde ne a zaben 2019 saboda Olaniyan.

Kara karanta wannan

2023: Ana Kokarin Kawo Karshen Rikicin Jam’iyyar PDP, Atiku Ya Zauna da Wike

Sun bayyana hakan ne a ranar Talata, 2 ga watan Agusta, a lokacin da Teslim Folarin, dan takarar gwamna na jam'iyyar APC da Olaniyan suka ziyarci garin tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.