Rashawar Da Aka Yi a Gwamnatin Buhari Ta Fi Wanda Akayi Cikin Shekaru 16 Na Gwamnatin PDP, In Ji Bwala

Rashawar Da Aka Yi a Gwamnatin Buhari Ta Fi Wanda Akayi Cikin Shekaru 16 Na Gwamnatin PDP, In Ji Bwala

  • Tsohon jigon jam'iyyar APC, kuma mai magana da yawun Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa na PDP a 2023 ya ce zargin rashawa da ake yi wa dan takarar na PDP ba gaskiya bane
  • Bwala, cikin hirar da aka yi da shi ya ce tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya sa an yi wa Atiku binciken kwa-kwaf amma har yau ba a kai shi kotu an same shi da laifi ba
  • Ya cigaba da cewa rashawar da aka tafka a karkashin gwamnatin Shugaba Buhari ta fi wanda aka yi a tsawon shekaru 16 na gwamnatin jam'iyyar PDP don haka ba ma abin a rika kwantantawa bane

Lauya kuma mai sharhi kan harkokin yau da kullum, Daniel Bwala, ya ce rashawa ta fi yawa a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari fiye da shekaru 16 na gwamnatin PDP, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Oshiomhole Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Wa Magoya Bayan Peter Obi Idan Suka Ce Za Su Tanka Masa

Bwala, wanda aka nada shi mai magana da yawun Atiku Abubakar don zaben shugaban kasa na 2023, ya bayyana hakan ne yayin hira da aka yi da shi a Channel TV a shirin Politics Today.

Bwala
Rashawar Da Aka Yi a Gwamnatin Buhari Ta Fi Na Gwamnatin PDP Tsawon Shekaru 16, Tsohon Jigon APC, Bwala. Hoto: @ChannelsTV.
Asali: Twitter

Ya ce ya koma PDP ne saboda ita ce kadai jam'iyyar da ke da shirin hada kan Najeriya, yana mai cewa Atiku ne kadai dan takarar da ke da kwarewar da zai iya jagorantar kasar.

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mafi yawancin hukumomi a Najeriya da ke aiki kuma mutane suke amfana da su, Atiku Abubakar ya taimaka wurin kafa su.
"Ko wannan batun rashawa da muke ta magana, idan har a kasa ta demokradiyya muke zaune, wanda kotu ta yanke wa hukunci shine ya aikata rashawa. Kuma zargin rashawar, ka san cewa mafi yawancin yan takarar shugaban kasa ana bincikarsu?

Kara karanta wannan

Buhari: Mun Ba Wa Jami'an Tsaro Cikakken 'Yanci Su Kawo Karshen Ta'addanci

"A Amurka, an bincikar Joe Biden a yayin zabe. Obasanjo ya bincike Atiku fiye da kowa. Nuhu Ribadu ya yi ta bincike don nemo hujja har yau babu ita. Amma muna cigaba da maganan rashawa.
"Ko ka san cewa rashawar da aka gano cikin shekara bakwai a wannan gwamnatin ya fi rashawar da aka gano daga 1999 zuwa yau? Dasuki dalla biliyan 2 ne; an shafe kusan shekaru 6 ana bincike. Idan ka dauki zargin rashawa biyu a gwamnatin nan za ta fi dala biliyan 2."

Atiku: Tikitin Musulmi Da Musulmi Yasa Ban Amince Da Tinubu Ba Lokacin Da Yake Son Zama Abokin Takara Na

A wani rahoton, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce kauracewa tikitin musulmi da musulmi yasa ya ki yarda Asiwaju Bola Tinubu ya yi masa mataimaki a zaben shekarar 2007, The Cable ta rahoto.

Atiku, wanda ya yi wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo mataki daga 1999 zuwa 2007, ne ya bayyana haka yayin wata hira da aka yi da shi a ARISE TV a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Baba-Ahmed Ya Bayyana Matsayar Peter Obi A Kan Kungiyar IPOB Ta Nnamdi Kanu

Atiku ya samu matsala da Obasanjo a yunkurinsa gadon kujerarsa, amma daga baya ya samu tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Action Congress, AC, jam'iyyar da Tinubu ya taimaka wurin kafa ta bayan 'guguwar' siyasa ta tarwatsa gwamnonin AD da aka zaba a 1999.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164