Oshiomhole Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Wa Magoya Bayan Peter Obi Idan Suka Ce Za Su Tanka Masa

Oshiomhole Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Wa Magoya Bayan Peter Obi Idan Suka Ce Za Su Tanka Masa

  • Sunan tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya dawo bakunan mutane a kafafen watsa labarai saboda maganan da ya yi
  • Tsohon shugaban na NLC kuma tsohon gwamnan Jihar Edo, yayin hira da shi da aka yi a talabijin ya soki yan takarar shugaban kasa inda ya ce sun gaza bayyana shirin da suke yi wa Najeriya
  • Ya kuma ware dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Mr Peter Obi, a matsayin daya cikin wadanda suka gaza bayyana tsare-tsaren da suka tanada wa kasar

Tsohon shugaban jam'iyyar APC mai mulkin kasa, Adams Oshiomhole, ya sha alwashin ba zai daga wa magoya bayan dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi, kafa ba idan suka tanka masa, Vanguard ta rahoto.

Adams Oshiomhole.
Oshiomhole Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Wa Magoya Bayan Peter Obi Idan Suka Tanka Masa. Hoto: Adams Oshiomhole.

Oshiomhole, direkta janar na kungiyar yakin neman zabe na Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta yayin hira da aka yi da shi a shirin Arise TV mai suna 'Morning Show'.

Kara karanta wannan

Garabasa: Matashi ya sa an yi layi, yana yiwa jama'a aski kyauta saboda kaunar Peter Obi

Tsohon gwamnan na jihar Edo ya kuma ce mafi yawancin masu neman takarar shugabancin kasar ba su fayyace tsarin da za su bi don warware matsalolin kasar ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Oshiomhole ya kama sunan Obi

Ya kara da cewa dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi, a matsayin misalin dan takarar da ya ki bayyana shirin da ya ke yi wa kasar.

Yayin hirar da aka yi da shi, an fada wa Oshiomhole cewa magoya bayan Obi za su yi ca a kansa saboda sukar dan takararsu, Oshiomhole ya bada amsa da cewa, "Ba zan raga musu ba."

Ya bayyana cewa babu wani amfani yin gaggawa, yana mai cewa, "wadanda suka yi gaggawan abin da suke son yi, sun yi bayyanin yadda za su yi abin,"

Oshiomhole ya ce zamanin da ya yi wa al'umma hidima don kwato hakkinsu babu wayoyin salula.

Kara karanta wannan

Elrufai Ya Ce APC ta Riga Ta Nada Darakata Janar Na Kamfen Din Takarar Tinubu Da Shettima

Kazalika, ya ce nan gaba za a gane ko magoya bayan Obi suna da biyayya kamar yadda suke ikirari idan zabe ya zo.

2023: Tikitin Musulmi Da Kirista Da Muka Yi A Baya Bai Tsinana Mana Komai Ba, Oshiomhole

A wani labarin, tsohon Gwamna Jihar Edo kuma tsohon shuganban APC na kasa, Adams Oshiomhole ya yi watsi da koken da wasu ke yi kan zaben musulmi a matsayin abokin takara da Ahmed Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasar jam'iyyar ya yi.

Oshiomhole ya ce lokaci ya yi a kasar da za a yi watsi da son zuciya da kuma abin da zuciya ke ji irin addini da kabilanci a mayar da hankali kan cancanta domin ceto kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel