2023: Yadda Rikicin PDP a Kano Zai Jefa Atiku da Jam’iyya a Barazana - Abacha

2023: Yadda Rikicin PDP a Kano Zai Jefa Atiku da Jam’iyya a Barazana - Abacha

  • Mohammad Sani Abacha ya fitar da jawabi bayan Jam’iyyarsu ta PDP ta bada sunan Sadiq Wali
  • PDP ta gabatar da sunan Wali a gaban INEC, hakan na nufin ba Abacha ba ne ‘dan takarar Gwamna
  • Kwamitin yakin neman zaben Abacha yace hukuncin da kotu tayi, ya jefa PDP a tsaka-mai-wuya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Mohammad Sani Abacha mai neman takarar gwamnan jihar Kano a PDP, yace burin Atiku Abubakar na zama shugaban kasa na fuskantar kalubale.

A ranar Litinin, 1 ga watan Agusta 2022, Daily Trust ta rahoto Mohammad Sani Abacha wanda jam’iyyar PDP ta ki yarda da takararsa, yana wannan bayani.

Ana rigima a PDP ta jihar Kano tsakanin bangaren Mohammad Sani Abacha da na Sadiq Wali.

Mohammed Abacha yana da goyon bayan shugaban PDP na Kano, Shehu Wada Sagagi yayin da shi kuma Sadiq Wali ke tare da tsagin Bello Hayatu Gwarzo.

Kara karanta wannan

Wike ya Zauna da Gwamnonin PDP, ya Gindaya Sharadin Marawa Atiku Baya

Shugaban INEC na kasa, Mahmood Yakubu ya shaidawa ‘yan jarida da farko sun san da zaman Abacha, amma PDP ta gabatarwa hukumar zabe wani 'dan takara.

Farfesa Mahmood Yakubu yace ana daf da karbar sunayen ‘yan takara sai bangaren Sanata Bello Gwarzo suka samu wata nasara a kotu da ta canza lissafin 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar a Kano Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Martanin Maniru Mailafiya

Da yake jawabi, Kakakin kwamitin yakin neman zaben Abacha, Maniru Mailafiya yace hukumar INEC tana magana ne a kan hukuncin kotun daukaka kara.

Babban kotun ya yi watsi da hukuncin da Alkalan kotun tarayya suka yi a game da bangaren da zai shiga zaben fitar da ‘dan takaran shugabancin kasa a PDP.

Maniru Mailafiya yake cewa hukuncin da kotun daukaka kara ya yi na nufin an ruguza duk kuri’ar ‘ya ‘yan jam’iyya na Kano da suka shiga zaben tsaida gwani.

Kara karanta wannan

Ana Tonon Silili, An Fara Fadan ‘Yan APC da Suka Hana Osinbajo Samun Takaran 2023

A lokacin zaben tsaida ‘dan takaran shugaban kasa, ‘yan tsagin Shehu Sagagi ne aka ba damar kada kuri’a, uwar jam’iyya ba ta amince da su Sanata Gwarzo ba.

A karshe, an ji Mailafiya yana mai kira ga INEC da ta amince da Abacha a matsayin cikakken ‘dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Takarar NNPP a Kaduna

An ji labari Sanata Suleiman Othman Hunkuyi yace da zarar Jam’iyyar NNPP ta karbi mulki a Kaduna, za a soke tsare-tsaren da gwamnatin APC mai-ci ta kawo.

Gwamna Nasir El-Rufai ya cirewa Hakimai 313 da Masu unguwanni 4, 453 rawani, sannan ya kara kudin karatu a manyan makarantun da ke jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel