Za Mu Dawo da Duk Sarakunan da Gwamnatin APC ta tsige Inji Jam’iyyar NNPP

Za Mu Dawo da Duk Sarakunan da Gwamnatin APC ta tsige Inji Jam’iyyar NNPP

  • Suleiman Othman Hunkuyi ya yi alkawarin zai maidawa Sarakunan da aka cire a Kaduna da rawaninsu
  • Sanata Suleiman Othman Hunkuyi yace zai janye karin kudin manyan makarantu da aka yi a fadin jihar
  • ‘Dan takaran na NNPP ya na sa rai Jam’iyyar hamayyarsa ta lashe zabuka a Kaduna a shekarar 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Suleiman Othman Hunkuyi mai neman Gwamna a jihar Kaduna, yace idan jam’iyyar NNPP ta yi nasara, za ta dawo da Sarakunan da aka tunbuke.

A ranar Lahadi, 31 ga watan Yuli 2022, Daily Trust ta rahoto Suleiman Othman Hunkuyi yana kamfe da Sarakunan da gwamnati mai-ci ta cirewa rawani.

Gwamnatin Nasir El-Rufai ta tsige Hakimai 313 da Masu unguwanni 4, 453 a shekarar 2017 a yunkurin yi wa masarautun da ke jihar Kaduna garambuwal.

Kara karanta wannan

Wike ya Zauna da Gwamnonin PDP, ya Gindaya Sharadin Marawa Atiku Baya

Nasir El-Rufai ya fahimci kudin da wadannan Sarakai suke ci ya yi yawa, don haka ya tunbuke su domin gwamnati ta samu kudin da za tayi wa al’umma aiki.

Za mu maida masu rawaninsu - NNPP

Da ya zanta da manema labarai a karshen makon da ya wuce, Sanata Suleiman Othman Hunkuyi yace zai dawo da wadannan mutane da zarar ya shiga ofis.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An rahoto Sanata Suleiman Othman Hunkuyi yana cewa zai yi hakan ne saboda irin rawar da sarakuna ke takawa wajen wanzar da zaman lafiya a al’umma.

Jam’iyyar NNPP
Rabiu Musa Kwankwaso da Suleiman Othman Hunkuyi Hoto: @mohd.saifullahi.9
Asali: Facebook

Hunkuyi zai rage kudin makarantu

Hunkuyi ya kara da cewa gwamnatinsu ta NNPP za ta janye karin kudin makarantar da El-Rufai ya yi, yace makarantu ba wuraren samun kudin shiga ba ne.

Har ila yau ‘dan takaran na jam’iyyar NNPP mai adawa ya koka a game da yadda gwamnatin APC ta bar jihar Kaduna da bashin fiye da Naira biliyan 300 a yau.

Kara karanta wannan

Gwamna El-Rufai ya rantse zai sallami duk Malaman Jami’a da ke yajin-aikin ASUU

A cewar Hunkuyi, bashin zai iya zarce wannan adadi idan aka yi la’akari da yadda aka karya Naira. Jaridar Premium Times ta kawo wannan rahoto a jiya.

Muddin NNPP ta kafa gwamnati a jihar Kaduna, Sanata Suleiman Hunkuyi yace zai maida hankali wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro da ake fama da shi.

Tsohon Sanatan ya nuna yana sa ran NNPP za ta karbe mulki a Kaduna a 2023, yake cewa suna da ‘yan takara da za su nemi kujeru 54 da ake da su a fadin jihar.

Musulmi-Musulmi da rigimar APC

Mun fahimci cewa rikicin da ake yi a jam’iyyar APC a kan tikitin Musulmi-Musulmi da aka yi a zaben 2023 ya jawo ana wasan tonon silili na cikin gida.

Ana zargin cewa Babachir Lawal da Yakubu Dogara sun yi wa Bola Tinubu aiki ne a APC, suka hana Yemi Osinbajo samun takara, yanzu suke yin nadama.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Da Yan Ta'adda Na Shirin Kai Hari Legas, Abuja, Katsina Da Wasu Jihohi 3, In Ji NSCDC

Asali: Legit.ng

Online view pixel