Da Ɗumi-Ɗumi: Jam'iyyar APC ta lashe Zaɓen kananan hukumomin Ebonyi

Da Ɗumi-Ɗumi: Jam'iyyar APC ta lashe Zaɓen kananan hukumomin Ebonyi

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Ebonyi, ta bayyana APC a matsayin jam'iyyar da ta lashe kujerun shugabannin kananan hukumomin 13 na jihar
  • Har ila yau, jam'iyyar mai mulki bata sassauta ba, ta samu nasarar kawo dukkan kujeru 171 na kansilolon gundumomin jihar baki daya
  • Shugaban EBSIEC, Jossy Eze, ya ce sun gamsu da sakamakon kuma sun yaba wa masu kada kuri'a kan yadda suka yi zaben gaskiya mai tattare da lumana

Ebonyi - Hukumar zabe ta jihar Ebonyi ta bayyana 'yan takarar APC a matsayin wadanda suka yi nasarar lashe dukkan kujerun shuwagabannin kananan hukumomin jihar da aka yi a ranar Asabar.

Hukumar ta ce, jam'iyyar mai mulki ta samu nasarar lashe kujeru 13 na kananan hukumomin jihar, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jigon Arewa: Babu gwamnatin da talakawa suka sha jar miya kamar ta Buhari

Jam'iyya APC
Da Ɗumi-Ɗumi: Jam'iyyar APC ta lashe Zaɓen kananan hukumomin Ebonyi. Hoto daga @thecableng
Asali: Twitter

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar, EBSIEC, Jossy Eze, ya yi wannan sanarwar a Abakaliki a ranar Lahadi a hedkwatar hukumar.

Kamar yadda Eze yace, APC ta lashe kujerun ciyamomi 13 da na kansiloli 171 a fadin jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa, ya yabawa masu kada kuri'a kan yadda suka yi zabe cike da kwanciyar hankali da zaman lafiya.

"Da karfin ikon da aka bani a shari'ance, ina bayyana sakamakon zabukan kananan hukumomi 13 kamar haka:
"A Abakaliki, Ebere Nwogba na jam'iyyar APC ya cika dukkan sharuddan da shari'a ta tanadar kuma ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben kuma ya tabbata wanda ya ci zaben."

Sauran 'yan takarar da suka ci zaben karkashin jam'iyyar APC sun hada da Chinedu Uburu na karamar hukumar Ebonyi, Chidiebere Uzor na karamar hukumar Onicha, Chinonsi Ajah na karamar hukumar Ohaozara, Ibiam Nnajiofor na karamar hukumar Afikpo ta arewa kuma Ekuma-Nkama Chima na karamar Afikpo ta kudu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wani rahoton sirri ya fallasa, 'yan ta'adda sun tara makamai za su afkawa jihar Buhari

"Hukumar ta karba kuma ta amince da sakamakon zabukan kansiloli 171 na gundumomin jihar. Hakan na nuna cewa APC ta lashe zabukan dukkan gundumomin," ya kara da cewa.

Wata mazauniya jihar mai suna Mary Apoke, wacce ta zanta da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, ta koka kan wannan cigaban inda tace zaben an yi ne don jam'iyya daya kacal.

"Ni kaina na fita zabe amma ban san sauran masu takara ba dake neman kujerar a sauran jam'iyyu banda APC, hakan ne yasa aka dinga yin bangare daya a zaben," Akpoke tace.

Emma Nweke, wani malamin makaranta, ya koka kan yadda aka yi zaben inda aka dinga nuna fifiko kan jam'iyyar APC mai mulki.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayyana cewa, jam'iyyar APGA da sauran jam'iyyun siyasa sun kauracewa zaben kananan hukumomin.

A wani labarin kuma Na Kusa Da Gwamna Tambuwal Da Wasu Jiga-Jigai Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC

Kara karanta wannan

Dillalan jakuna: 'Yan Najeriya miliyan 3 za su rasa sana'a idan aka hana yanka jakuna

Makusancin Gwamnan jihar Sokoto kuma shugaban karamar hukumar Tangaza, Isah Bashar Kalanjine, ya bar jam'iyyar PDP zuwa APC.

Makusancin Gwamna Tambuwal din ya kara da yin tsarabar kansilolin karamar hukumarsa takwas zuwa jam'iyya mai mulkin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262