Mataimakin kakakin majalisa: Babu wata gwamnati da ta taimaki talakawa kamar ta APC

Mataimakin kakakin majalisa: Babu wata gwamnati da ta taimaki talakawa kamar ta APC

  • Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Idris Wase, ya yi amanna da cewa jam’iyya mai mulki, APC ita ce mafi alherin abin da ya taba faruwa da ‘yan Najeriya
  • Ya bayyana cewa APC ta fi taigmakon rayukar talaka fiye da yadda wasu gwamnatoci suka yi mulki a kasar nan
  • Hakazalika, Wase ya bukaci magoya bayan jam’iyyar da su ci gaba da marawa Bola Tinubu baya a yunkurinsa na neman kujerar Buhari

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja – Mataimakin kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Idris Wase, ya ce jam’iyyar APC mai mulki ta fi taimakon rayukar talaka fiye da yadda wasu gwamnatoci suka yi a baya.

Kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito, mataimakin shugaban majalisar ya yi wannan ikirarin ne a ranar Laraba, 27 ga watan Yuli a Abuja yayin da yake karbar tawagar yakin neman zaben Bola Tinubu a majalisar dokokin kasar.

Kara karanta wannan

Ku kiyayi Abuja, akwai matukar hatsari a cikinta: 'Dan majalisa ya gargadi abokan aikinsa

APC ta taimake talaka a Najeriya
Mataimakin kakakin majalisar: Babu wata gwamnati da ta taba rayuwar talakawan kasa kamar ta APC | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Yace:

“Babu wata gwamnati da ta taimaki rayuwar talakawan Najeriya wadanda ba su da abin yi - wadanda suka kammala karatun digiri, manya, matasa - ta fuskar abubuwan more rayuwa daban-daban da aka ba su, kamar yadda gwamnatin APC ta yi. Burinmu shi ne mu karfafa kan wadannan.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit.ng ta tattaro cewa kungiyar mayoya bayan Tinubu a zaben 2023 sun yi wannan ziyara ne a wani yunkuri na neman goyon bayan mataimakin kakakin majalisar domin ganin Bola Tinubu ya samu nasara a zaben shugaban kasa na 2023.

Mataimakin shugaban majalisar ya ce:

“Majalisar wakilai, musamman ‘yan jam’iyyar APC, za su hada kai da kowace kungiya domin tabbatar da nasarar tikitin Tinubu/Shettima.
“Muna da haja mai kyau da za mu sayar; wannan shi ne wanda ya habaka tattalin arzikin Legas cikin kankanin lokaci ya kuma gina jama’a a fadin kasar nan ba tare da la’akari da yanki ko addini ba.”

Kara karanta wannan

Wasu Jihohi 16 Za Su Iya Fusakantar Yunwa da Karancin Abinci inji ‘Yan Majalisa

2023: Ana iya siyar da Tinubu – Mataimakin kakakin majalisa

Hakazalika, ya bukaci kungiyar goyon bayan da ta yi wa tsohon gwamnan jihar Legas goyon baya da kuma hada kan masu kada kuri’a da karfi don tabbatar da damar Tinubu.

Wase ya bayyana Tinubu a matsayin wata haja mai kyau da za a iya siyar da ita ga jama’a yayin da ya yi tsokaci kan kwazonsa da ya yi a matsayinsa na gwamnan jihar Legas ta fuskar bunkasar tattalin arziki.

Yace:

“Ina ta maimaitawa; babu wani dan takara a kowace jam’iyyar siyasa da zai yi daidai da ingancin takarar jagora Ahmed Bola Tinubu."

Ya bayyana cewa, ya kamata 'yan APC su yi duk mai yiwuwa domin tara wa Tinubu kuri'u a zaben 2023.

Ya kuma ba da tabbacin cewa, mambobin jam'iyyar a fadin Najeriya za su kawo kuri'u masu yawa.

Ya ce:

"Ina so in tabbatar muku da cewa da yardar Allah, APC za ta zo da adadi mai yawa ta fuskar goyon baya."

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa tayi Martani Mai Zafi ga Sanatocin da ke Yunkurin tsige Buhari

Wase ya kara da cewa gwamnati mai ci ta yi duk mai yiwuwa wajen biyan bukatun marasa galihu a Najeriya kamar yadda ake yi a sauran kasashen duniya.

A nasa bangaren, kodinetan kungiyar na kasa, Oyinkansola Okiwuyi ya nuna jin dadinsa ga yadda mataimakin shugaban majalisar ganin yadda ya bayyana kwarin gwiwarsa ga taifyar Tinubu.

Atiku da Tinubu sun Gamu da Cikas, Tsohon Ministan Buhari Yace Shi ne ‘Dan takara

A wani labarin, tsohon Ministan ilmin Najeriya, Chukwuemeka Nwajiuba da wata kungiya sun shigar da kara a kan Asiwaju Bola Tinubu da Alhaji Atiku Abubakar.

Lauyoyin tsohon Ministan da na Incorporated Trustees of Rights for All International suna so a ayyana Chukwuemeka Nwajiuba a matsayin ‘dan takaran APC.

Punch tace an shigar da wannan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/942/22 ne a kotun tarayya na Abuja. Mutane shida da ake kara sun hada da jam’iyyun APC da PDP, Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Babban Lauyan Gwamnati da kuma hukumar zabe watau INEC.

Kara karanta wannan

Za Mu ba ‘Yan Najeriya Mamaki a Zaben 2023 inji Abokin takarar Kwankwaso

Asali: Legit.ng

Online view pixel