Yanzu-Yanzu: Tsohon jigon jam'iyyar APC a jihar Ribas ya yi wanka, ya koma SDP
- Jigon jam'iyyar APC a jihar Ribas ya tabbatar da komawarsa jam'iyyar SDP mai alamar doki da ke fara tashe
- Magnus Abe ya bayyana cewa, zai yi takarar gwamna duk da kuwa bai halarci wani zaben fidda gwani da aka yi ba
- An samu jiga-jigan jam'iyyun siyasan kasar nan da suka sallama, kana suka sauya sheka zuwa wasu jam'iyyun
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Ribas - Daga karshe dai tsohon wakilin Ribas ta Kudu maso Gabas a majalisar dokokin kasa, Sanata Magnus Abe ya tabbatar da sauya sheka zuwa jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Party Benson ya fitar, tsohon dan jam’iyyar ta APC ya tabbatar da hakan a shafinsa na sada zumunta, The Nation ta ruwaito.
Abe ya nanata kudurinsa na tsayawa tsayin daka kan manufar da ya yi imani da shi, don inganta dimokuradiyyar cikin gida don ci gaban mulkin al'umma.
Abe, wanda ya fice daga jam’iyyar APC a makon da ya gabata, ya bayyana cewa yana neman tsarin siyasa ne mai kyau domin ya cika burinsa na maye gurbin Gwamna Nyesom Wike a 2023.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce:
Eh ni ne kuma na kasance dan jam’iyyar Social Democratic Party SDP.
“Zan ci gaba da jajircewa kan manufofin da suka kawo tafiyar siyasar ta tsawon shekaru. Kuma za mu ci gaba da yin duk mai yiwuwa don inganta dimokuradiyyar cikin gida a siyasar kasarmu ta tabbatar da mayar da hankali kan jama’a”.
Abe ya ci gaba da tabbatar da cewa zai tsaya takarar gwamna duk da cewa bai halarci zaben fidda gwani na wata jam'iyya ba, PM News ta kawo.
Jam’iyyar SDP ta zabi Maurice Prunem, dan tsagin Abe kuma dan asalin karamar hukumar Tai, a matsayin dan takararta na gwamnan Ribas.
Mataimakin kakakin majalisa: Babu wata gwamnati da ta taimaki talakawa kamar ta APC
A wani labarin, mataimakin kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Idris Wase, ya ce jam’iyyar APC mai mulki ta fi taimakon rayukar talaka fiye da yadda wasu gwamnatoci suka yi a baya.
Kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito, mataimakin shugaban majalisar ya yi wannan ikirarin ne a ranar Laraba, 27 ga watan Yuli a Abuja.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar tawagar yakin neman zaben Bola Tinubu a majalisar dokokin kasar.
Asali: Legit.ng