Dan Takarar Gwamnan Zamfara A Jami'iyyar PDP Ya Kai Wa Atiku Ziyarar Ban Girma

Dan Takarar Gwamnan Zamfara A Jami'iyyar PDP Ya Kai Wa Atiku Ziyarar Ban Girma

  • Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya tabbatar wa Dauda Lawal cewa PDP zata yi kokarin lashe zaben jihar Zamfara
  • Atiku Abubukar ya ce Abin da ya fi dacewa a yi wa al’ummar Jihar Zamfara shi ne a samar da zaman lafiya, kare gonaki, da inganta kasuwanci
  • Dauda Lawal ya ce yan Najeriya suna kewan jam'iyyar PDP saboda kunchi da jam'iyyar APC ta saka su a ciki na rashin iya shugabanci

Jihar Zamfara - Atiku Abubakar, ya tabbatar wa dan takarar gwamnan jihar Zamfara na jam’iyyar PDP, Dr. Dauda Lawal cewa zai yi kokarin ganin jam’iyyar PDP ta lashe zaben 2023 a jihar. Rahoton LEADERSHIP

Tsohon mataimakin shugaban kasar na magana ne a gidansa da ke Abuja ranar Laraba lokacin da Lawal ya jagoranci mambobin jami’yyar PDP da masu ruwa da tsaki a jihar suka kai wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ziyarar ban girma.

Kara karanta wannan

Fasto Tunde Bakare Yayi Bayani akan goyon Bayan Tinubu da Sukar Kungiyar CAN Da aka Ce Yayi

A cewar Atiku, abin da ya fi dacewa a yi wa al’ummar Jihar Zamfara shi ne a samar da zaman lafiya, kare gonaki, da inganta kasuwanci.

Atiku
Dan Takarar Gwamnan Zamfara A Jami'iyyar PDP Ya Kai Wa Atiku Ziyarar Ban Girma FOTO LEADERSHIP
Asali: UGC

Amma Dole ne mu kwace mulki daga APC don ceto ta da sake gina jihar da kasa baki daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar gwamnan jihar Zamfara a PDP, kuma tsohon babban darakta a bankin First Bank,ya bayyana cewa ‘yan Najeriya a yanzu suna kewar jam’iyyar PDP saboda kunci da suka shiga na rashin iya shugabancin jam’iyyar APC mai mulki.

Atiku Da Gwamna Okowa Sun Gana Da Sanatocin PDP A Kokarin Rarrashi

A wani labari kuma, Mambobin jam'iyyar PDP da ke majalisar dattawan Najeriya sun gana da ɗan takarar jam'iyyarsu na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da ɗan takarar mataimaki, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ranar Talata.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa an gudanar da taron ne a wani ɓangare na rarrashin mambobin jam'iyya waɗan da suka fusata domin tunkarar babban zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel