Gwamnan PDP: Atiku ya sharara wa 'yan Najeriya karairayi a wata tattaunawa
- Gwamnan jihar Ribas ya tono wani batu mai ban mamaki kan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP
- Nyesom Wike ya bayyana cewa, Atiku ya tafka karairayi a gidan talabijin game da yadda tsakaninsa yake da dashi
- Tun bayan zaben fidda gwanin shugaban kasa na PDP aka samu tsaiko tsakanin Atiku Abubakar da Nyesom Wike
Fatakwal, jihar Ribas - Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya sharara karya da dama yayin hirar da aka yi da shi kwanan nan, rahoton The Nation.
Wike, wanda ya yi magana da safiyar yau Juma’a a filin jirgin sama na Fatakwal, ya ce:
“Bayan nan (Atiku) ya bayyana a gidan talabijin na Arise, ga irin kalaman da ya yi. Tarin karairayi da yawa.”
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A hirar da Wike ke magana a kai, Atiku ya ce bai zabi Wike a matsayin abokin takararsa ba saboda yana son wanda zai yi aiki da shi cikin aminci, rahoton TheCable.
Atiku: Banyi Watsi Da Wike Ba, Na zabi Dan Takarar Da Zan Iya Aiki Da Shi ne
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce bai zabi Nyesom Wike, gwamnan Rivers, a matsayin abokin takararsa ba, saboda yana son wanda zai yi aiki da shi cikin aminci.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da yayi da Arise TV ranar Juma'a.
Dan takarar na PDP ya zabi Ifeanyi Okowa, gwamnan Delta, a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023, duk da cewa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NWC) ta amince da Wike a matsayin mataimakinsa.
Zabin dai ya janyo matsala a cikin jam'iyyar, inda wasu gungun masu ruwa da tsaki suka dage cewa a dauki Wike.
Da yake magana akan zabin dan takarar mataimakin shugaban kasa, Atiku yace ya zabi Okowa ne maimakon Wike saboda yana son wanda zai iya sadar da manufofin jam’iyyar.
Mataimakin kakakin majalisa: Babu wata gwamnati da ta taimaki talakawa kamar ta APC
A wani labarin, mataimakin kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Idris Wase, ya ce jam’iyyar APC mai mulki ta fi taimakon rayukar talaka fiye da yadda wasu gwamnatoci suka yi a baya.
Kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito, mataimakin shugaban majalisar ya yi wannan ikirarin ne a ranar Laraba, 27 ga watan Yuli a Abuja.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar tawagar yakin neman zaben Bola Tinubu a majalisar dokokin kasar.
Asali: Legit.ng