Atiku Da Gwamna Okowa Sun Gana Da Sanatocin PDP A Kokarin Rarrashi

Atiku Da Gwamna Okowa Sun Gana Da Sanatocin PDP A Kokarin Rarrashi

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya fara koƙarin rarrashin mambobin jam'iyya gabanin zaɓen 2023
  • A wani babban yunkuri, Atiku da abokin takararsa sun gana da Sanatocin PDP domin shawo kan waɗan da suka fusata
  • Babbar jam'iyyar hamayya ta shiga rikici ne tun bayan kammala zaɓen fidda gwani wanda Atiku ya lashe

Abuja - Mambobin jam'iyyar PDP da ke majalisar dattawan Najeriya sun gana da ɗan takarar jam'iyyarsu na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da ɗan takarar mataimaki, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ranar Talata.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa an gudanar da taron ne a wani ɓangare na rarrashin mambobin jam'iyya waɗan da suka fusata domin tunkarar babban zaɓen 2023.

Atiku, Okowa da Ayu.
Atiku Da Gwamna Wike Sun Gana Da Sanatocin PDP A Kokarin Rarrashi Hoto: channelstv
Asali: UGC

Atiku ya rubuta a shafinsa na Tuwita cewa:

"A daren jiya, abokin takara na, shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, da ni kaina mun gana da Sanatocin jam'iyyar mu karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye, Sanata Philip Aduda."

Kara karanta wannan

Gwamnoni arewa uku da wasu jiga-jigan APC sun sa labule da Tinubu, Shettima a Abuja

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Manyan jiga-jigan babbar jam'iyyar hamayya kamar irin Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, sun nuna ƙarara ba su jin daɗin cigaban da ake samu a PDP.

Gwamna Wike ya sha kaye a zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa wanda Atiku Abubakar ya lashe, haka nan kuma an tsallake shi lokacin zaɓo ɗan takarar mataimaki.

Bayan Wike, ɗaya daga cikin masu faɗa aji na PDP, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, ya nuna damuwarsa kan yadda ake yi wa gwamnan Ribas rashin adalci.

Ortom ya bayyana cewa ya kamata ace an nemi shawararsa kafin ɗaukar matakin zaɓo gwamna Okowa a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP.

Zamu rarrashi mambobi - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya sha alwashin haɗa kan jam'iyyar gabanin zuwan babban zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

'Zaka sha mamaki' Peter Obi ya maida zazzafan martani ga Atiku Abubakar kan zaɓen 2023

Daga cikin waɗan da suka halarci taron wanda ya gudana ranar Talata har da shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu.

Hotunan taron

Taro da Sanatocin PDP.
Atiku Da Gwamna Wike Sun Gana Da Sanatocin PDP A Kokarin Rarrashi Hoto: channelstv
Asali: UGC

Atiku da Babba Kaita.
Atiku Da Gwamna Wike Sun Gana Da Sanatocin PDP A Kokarin Rarrashi Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

Taro da Sanatoci.
Atiku Da Gwamna Wike Sun Gana Da Sanatocin PDP A Kokarin Rarrashi Hoto: channelstv
Asali: UGC

A wani labarin kuma kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na LP Peter Obi ya maida zazzafan martani ga Atiku Abubakar kan zaɓen 2023

Tsohon gwamnan Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa ya ce ya ƙosa ya ba da mamaki a babban zaɓen 2023.

Peter Obi, yayin martani ga kalaman Atiku Abubakar na PDP, ya ce dama can rayuwar siyasarsa cike take da abubuwan Al'ajabi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel