Kanin Gwamnan APC Ya Ce Baya Son Mukamin Da Buhari Ya Nada Shi A RMAFC, Ya Ce Mai So Ya Tafi Ya Nema
- Augustine Umahi, kanin Gwamna Dave Umahi na Jihar Ebonyi, ya ki karbar nadin da Shugaba Muhammadu Buhari ya masa a matsayin sakataren hukumar RMAFC
- A baya-bayan ne Shugaba Muhammadu ya yi sabbin nade-naden uku ciki har da nadin Augustine Umahi amma da ya yi godiya ya kuma ce ba zai iya karbar nadin ba
- Augustine ya ce a shekarunsa da kwarewarsa na aiki ya san abin da ya ke so a rayuwa don haka ba zai karbi nadin ba ya kuma shawarci duk wani mai son mukamin ya tuntubi Gwamna Umahi
Jihar Ebonyi - Augustine Umahi ya ki karbar mukamin da aka bashi a matsayin sakatare na Hukumar Rarraba Kudaden Shiga da Kasafin Kudi, RMAFC, rahoton Daily Trust.
Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Laraba ya amince da nadin mutane uku a hukumomin gwamnati a matsayin shugabanni.
Mr Umahi na cikinsu, wanda zai yi aiki a matsayin sakataren RMAFC na wa'adin farko na shekaru hudu da zai fara daga ranar 6 ga watan Yuli.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Amma, Umahi, wanda kani ne na Gwamna Dave Umahi na Jihar Ebonyi, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Abakaliki, ya ce bai karbi nadin ba.
"Na yi godiya bisa kauna da aka nuna min amma ina nadamar sanar da kai cewa ba zan amince da nadin ba.
"Hakan kuma shine domin ya fi dacewa da masu neman aiki, ma'aikatan gwamnati da suka yi murabus ko duk wani mai kaunar aikin.
"Na kuma gamsu cewa da shekaru na da kwarewar aiki, na san abin da na ke bukata a rayuwa.
"Duk wanda ke sha'awar mukamin, kada ya yi kasa a gwiwa ya tuntubi gwamna don yin abin da ya dace. Domin iya sani na, har yanzu babu wanda ya cike gurbin," in ji Umahi.
Umahi ya ci zaben fidda gwani na kujerar sanata a mazabar Ebonyi South karkashin jam'iyyar All Progressive Congress, APC, da aka yi a ranar 28 ga watan Mayun 2022.
An rahoto cewa ya janye wa gwamnan jihar Ebonyi matsayin bayan gwamnan ya gaza samun tikitin takarar shugaban kasa a APC.
Amma, jam'iyyar ta APC ta saka ranar yin zaben raba gardama a ranar 31 ga watan Yuli kamar yadda kotu ta umurta tana mai cewa gwamnan ba zai iya rike tikitin ba.
Shugaba Buhari Ya Yi Sabbin Naɗe-Naɗe Uku A Hukumomin Tarayya
Tunda farko, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da naɗin wasu mutum uku a matsayin shugabannin wasu hukumomin tarayya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Daraktan watsa labarai na Ofishin Sakataren gwamnatin tarayya, Mista Willie Bassey, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a birnin tarayya Abuja ranar Laraba.
Asali: Legit.ng