Shugaba Buhari Ya Yi Sabbin Naɗe-Naɗe Uku A Hukumomin Tarayya

Shugaba Buhari Ya Yi Sabbin Naɗe-Naɗe Uku A Hukumomin Tarayya

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da naɗin wasu mutum uku a matsayin shugabannin wasu hukumomin tarayya
  • Mutanen da shugaban ya naɗa sun haɗa da Tijjani Ƙaura, Mista Augustine Umahi da kuma Kaftin Junaid Abdullahi
  • Naɗin shugaban kasa na zuwa ne a dai-dai lokacin da Sanatocin jam'iyyun adawa suka ba shi wa'adi ya kawo karshen matsalar tsaro

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amiɓce da naɗin wasu mutum uku a matsayin shugabannin wasu hukumomin tarayya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daraktan watsa labarai na Ofishin Sakataren gwamnatin tarayya, Mista Willie Bassey, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a birnin tarayya Abuja ranar Laraba.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yana sa hannu.
Shugaba Buhari Ya Yi Sabbin Naɗe-Naɗe Uku A Hukumomin Tarayya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Waɗan da Allah ya ci da a sabon naɗin Buhari sun haɗa da Tijjani Ƙaura a matsayin shugaban hukumar 'yanta Mai da Gas, wanda zai fara zangonsa na farko na tsawon shekara uku daga 18 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sanatoci sun yi barazanar tsige shugaba Buhari, sun ba shi wa'adin mako 6

Sai kuma Mista Augustine Umahi wanda zai ɗare kujerar Sakataren hukumar wayar da kai kan haraji, rabo da kasafi, wanda ya fara zangon farko na shekara huɗu daga ranar 6 ga watan Yuli.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sanarwan, shugaban ƙasa ya sabunta naɗin Kaftin Junaid Abdullahi a matsayin shugaban hukumar raya yankunan da ke bakin iyaka ta ƙasa (BCDA).

Kaftin Junaid, bayan sabunta naɗinsa, zai shiga zangon mulkinsa na ƙarshe wanda zai shafe shekaru huɗu daga ranar 22 ga watan Satumba.

Legit.ng Hausa ta gano cewa Jiunaid Abdullahi, suruki ne ga shugaban kasa Buhari. Ya aure ɗiyarsa, Zulai, wacce ta rasu shekara 10 da ta gabata.

Ku zage dantse a aikin ku - Buhari

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta ruwaito wani sashin sanarwan na cewa:

"Shugaban kasa, Muhammadu Buhari. ya ta ya waɗan da aka naɗa murna kuma ya roke su da su yi amfani da kwarewar da Allah ya basu wajen tafiyar da kujerun su."

Kara karanta wannan

2023: Ka mutunta alƙawarin da ka ɗauka, Jigon APC ga Gwamnan PDP da ake raɗe-raɗin zai sauya sheƙa

A wani labarin kuma Dirama ta barke a majalisar Dattawan Najeriya, Sanatoci sun fusata bayan kawo batun tsige Buhari

Wata hatsaniya ta ɓalle a zauren majalisar dattawan Najeriya bayan fatali da bukatar tattauna wa kan tsige shugaba Buhari.

Shugaban marasa rinjaye, Sanata Aduda, ya bukaci majalisar ta tattauna kan matsalar tsaro da kuma tsige Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel