Rikici ya rincabe a NNPP, ‘Yan Jam’iyya sun bukaci ‘Dan takarar Gwamna ya sauka
- Yahaya Ibrahim Mohammed Sokodeke yana fuskantar barazana a takarar Gwamna da zai yi
- Shugabannin jam’iyyar NNPP daga jihar Neja sun taru, sun bukaci a hana shi shiga takaran 2023
- Sokodeke shi ne wanda NNPP ta ba tikitin neman Gwamna a Neja, amma ana jifarsu da laifuffuka
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Niger - Shugabannin jam’iyyar NNPP na reshen jihar Neja, sun bukaci ‘dan takarar gwamna, Yahaya Ibrahim Mohammed Sokodeke, ya janye takararsa.
A ranar Alhamis, 28 ga watan Yuli 2022, rahoto ya fito daga Daily Trust inda aka ji takarar Yahaya Ibrahim Mohammed Sokodeke tana fuskantar barazana.
Shugabanni 21 na jam’iyyar adawar a Neja sun rubuta wata wasika zuwa ga uwar jam’iyya da kuma jagora na kasa watau Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Kamar yadda rahoton ya bayyana, ‘yan jam’iyyar sun yi korafi a kan Alhaji Yahaya Sokodeke.
Wasikar shugabannin NNPP
Shugaban NNPP na Neja, Mamman G. Damisa da mataimakansa; Mohammed Kafinta, Ibrahim Kafinta da Awwal M. Gonna, sun sa hannu a wasikar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga zargin da shugabanninsa na jiha suke yi masa shi ne, kungiyoyi sun kawo karar ‘dan takararsu, suna zargin mai neman gwamnan da cin amana.
Damisa, Kafinta, Kafinta, Gonna da wasu mutane 17 sun ce idan aka kyale ‘dan takaran ya shiga zaben neman gwamna a 2023, NNPP za ta gamu da cikas.
Yadda abin yake - Hadimin Sokodeke
Amma ‘dan takaran ya maidawa shugabannin na sa martani ta bakin hadiminsa, Ahmed Aliyu Lanle, wanda ya yi magana da Legit.ng Hausa a safiyar Alhamis.
Ahmed Aliyu Lanle yake cewa ana fushi da mai gidansa ne saboda wasu sun nemi ya saida masu takararsa, shi kuma ya nuna sam bai da niyyar saida tikitinsa.
A cewar Lanle, uwar jam’iyya da kuma majalisar amintattun NNPP watau BOT, ba su amince da wannan bukata ba, kuma sun yi watsi da wasikar da aka rubuta.
INEC ta tabbatar da Talban Samarin Nupe a matsayin 'dan takaran NNPP. Lanle yace Sokodeke yana kokarin sasantawa da wadanda ya doke wajen samun tikiti.
Legit.ng Hausa ta fahimci Sokodeke ya dage wajen neman takaran da yake yi, kwanan nan zai kaddamar da babban ofishinsa na yakin neman zabe a Minna.
EFCC ta cafke Atiku, Tinubu - NNPP
A farkon makon nan aka ji labari jam’iyyar NNPP da ake yi wa kirari da mai kayan marmari tana so a hana PDP da APC takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Shugaban NNPP na Katsina yace bai kamata Atiku Abubakar da Bola Tinubu su nemi mulki ba domin an saba doka wajen tsaida su takara a zaben fitar da gwani.
Asali: Legit.ng