Za Mu ba ‘Yan Najeriya Mamaki a Zaben 2023 inji Abokin takarar Kwankwaso

Za Mu ba ‘Yan Najeriya Mamaki a Zaben 2023 inji Abokin takarar Kwankwaso

  • Bishof Isaac Idahosa yayi alkawarin cewa jam’iyyar NNPP za ta ba jama’a mamaki a zaben shugaban kasa
  • ‘Dan takarar mataimakin shugaban kasar na NNPP ya yi bayanin shirin da suke yi wa zaben mai zuwa
  • Isaac Idahosa yace shi da Rabiu Kwankwaso za suyi kokarin hada-kan al'umma, a yanzu da kai ya rabu

Abuja - Abokin takarar Rabiu Musa Kwankwaso a jam’iyyar NNPP, Isaac Idahosa ya yi wata hira ta musamman, inda ya yi bayanin shirin da suke yi.

Bishof Isaac Idahosa ya zanta da gidan talabijin na Channels TV a ranar Talata, 26 ga watan Yuli 2022, yace za su ba al’umma mamaki a zabe mai zuwa.

A tattaunawar da aka yi, ‘dan takarar mataimakin shugaban kasar yayi bayanin yadda NNPP tayi niyyar shawo kan matsalolin da suka yi katutu.

Kara karanta wannan

2023: Sanusi II ya yi Jawabi a Game da Zabe, ya Bayyana cikas 1 da ake Fuskanta

Da aka tambaye shi a game da yadda zai taimakawa NNPP a zaben shugaban kasa da kuma idan an yi nasarar lashe zaben, sai yace shi tsohon Fasto ne.

Isaac Idahosa ya bayyana cewa shekararsa 33 yana jagorantar Kiristoci a coci, baya ga aikin wa’azi, yace suna hulda da duk wasu masu zuwa yin ibada.

A ra’ayin malamin da ya zama ‘dan siyasa, ya samu kwarewa wajen mu’amalantar sauran kabilu, wanda yace ana bukatar wannan hadin-kan a yau.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abokin takarar Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso da Isaac Idahosa Hoto: mohd.saifullahi.9
Asali: Facebook

Faston yake cewa idan babu zaman lafiya da kwanciyar hankali, ba zai yiwu kasar ta cigaba ba, shiyasa suke yunkurin zaunar da kiristoci da musulmai.

Idahosa yana da nauyi a siyasa?

An tambayi Idahosa ko zai iya bugun kirji a kan mabiyansa da yawan kuri'un da zai kawowa NNPP a 2023, sai ya nuna yana zama da 'yan siyasa a cocinsa.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi alkawarin yiwa jama'arsa wani abin da Buhari ya gagara yiwa 'yan Najeriya

Bishof Isaac Idahosa yake cewa za su girgiza jama’a daga watan Satumban da za a soma kamfe domin neman zama shugabancin Najeriya a zaben 2023.

Idahosa ya fadawa abokin hirar ta shi cewa wadanda ba su yi imani da jam’iyyar NNPP da ‘yan takaran na ta ba, za su taya su murnar lashe zabe a 2023.

Za mu bada mamaki - Idahosa

“Za mu ba ‘Yan Najeriya mamaki, za su iya cewa abin ba zai yiwu ba, amma nan gaba za su taya mu murna.”
“Muna tattauna yanzu haka, kuma mun fara hangen yakin neman zabe, wanda zai girgiza masu shakka."

Sowore da Garba Shehu

A 'yan kwanakin nan aka ji labari Yele Sowore ya fallasa Garba Shehu, ya zarge sa da yi wa Gwamnatin Obasanjo zagon-kasa da yake aiki da Atiku Abubakar.

Da aka zanta da shi, Sowore mai neman zama Shugaban kasa a African Action Congress (AAC) ya bayyana alakarsa da Garba Shehu da bai taba fada ba.

Kara karanta wannan

Hotuna Da Bidiyoyin Ali Modu Sheriff Yana Nasiha Ga Diyar Danuwansa, Yacine da angonta Shehu Yar’adua

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng