Kwankwaso ya Ziyarci Jagoran Dattawan Arewa, an Bayyana Dalilin Ziyarar
- Rabiu Musa Kwankwaso da ‘yan tawagarsa sun kai ziyara zuwa gidan Farfesa Ango Abullahi
- ‘Dan takaran shugaban kasar ya yi wa Dattijon ta’aziyyar Isa Abdullahi wanda ya rasu kwanaki
- A baya an ji Shugaban kungiyar ta Dattawan Arewa ta NEF yana yabawa nagartar Kwankwaso
Kaduna - Rabiu Musa Kwankwaso wanda yake neman takarar zama shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar NNPP ya ziyarci Ango Abdullahi.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da tawagarsa sun kai wa Dattijon ziyara a gidansa da ke Zaria, jihar Kaduna a ranar Lahadi, 25 ga watan Yuli 2022.
Hadimin ‘dan siyasar, Saifullahi Hassan, ya wallafa hotunan haduwarsa da Farfesa Ango Abdullahi.
Kamar yadda Mai taimakawa Rabiu Musa Kwankwaso ya shaida a shafinsa na Twitter, tsohon gwamnan ya yi wa Ango Abdullahi ta’aziyyar 'dansa.
A kwanakin baya babban ‘dan Farfesa Abdullahi a Duniya, Malam Isa Isa Abdullahi ya rasu.
‘Dan takaran jam’iyyar hamayyar ya yi amfani da wannan dama wajen yi wa shugaban kungiyar NEF ta Datttawan Arewa ta’aziyyar wannan rashi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Baya ga hakan, Sanata Kwankwaso ya yi wa daukacin iyalin Farfesan addu’a, tare da yin kira gare su da sun rungumi kaddara domin kowa zai bar Duniya.
A karshe Kwankwaso ya yabawa Ango Abdullahi a kan irin rawar da yake takawa wajen ganin an tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa.
Bude ofisoshin NNPP
Legit.ng Hausa ta fahimci Kwankwaso ya zo jihar Kaduna a karshen makon da ya gabata, a nan ya kaddamar da wasu daga cikin ofisoshin jam’iyyar NNPP.
Wadanda suka yi wa Kwankwaso rakiya sun hada da Buba Galadima, ‘dan takarar Gwamnan Kaduna a zaben 2023, Sanata Sulaimen Othman Hunkunyi.
Gidan Magajin Rafin Zazzau da ke unguwar GRA a karamar hukumar Sabon Gari, ya cika da magoya bayan Kwankwaso da wasu shugabannin NNPP a ranar.
Peter Obi a Arewa
Kwanaki kun samu rahoto Mahadi Shehu ya ce makasudin zuwan Olusegun Obasanjo Arewa shi ne tallata takarar Peter Obi wanda ya tsaya a LP.
A wata hira da aka yi da shi, Mai kamfanin Dialogue Group ya ce tsohon shugaban kasa Obasanjo yana tare da Obi a zaben da za ayi a shekara mai zuwa.
Asali: Legit.ng