Mambobin APC da PDP 200 sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar LP a Abuja
- Jam'iyyar LP wacce Peter Obi ke takarar shugaban ƙasa ta samu gagarumin goyon baya a babban birnin tarayya Abuja
- Yayin da ake gab da fara yaƙin neman zaɓe, ɗaruruwan mambobin APC da PDP a yankin Kuje sun sauya sheƙa zuwa LP
- Ana hasahen zaɓen 2023 ka iya baiwa kowa mamaki ta yadda Obi ka iya yin abun al'ajabi
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Jam'iyyar Labour Party (LP), ranar Litinin, ta karɓi masu sauya sheƙa sama da 200 daga manyan jam'iyyun siyasa PDP da APC a gundumar Gaube, ƙaramar hukumar Kuje a birnin tarayya Abuja.
Daily Nigerian a rahoton ta tace masu sauya sheƙan, waɗan da suka miƙa tsintsiyoyi, laima, katin jam'iyya da fastoci, sun ce matakin ya zama wajibi a kansu domin Demokaraɗiyya ta gaske ta farfaɗo a kasar nan.
Auditan LP reshen Abuja, Fanimi Oluwabusayo, yayin bikin karɓan mutanen, ya tabbatar musu da cewa jam'iyyar ta zo ne domin ta ceto yan Najeriya daga ƙaƙanikayin da manyan jam'iyyu biyu suka jefa ƙasa.
Mista Oluwabusayo, wanda aka fi sani da Bigggy, ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"LP ta zo da cikakken karfin da zata sauya tarihin demokaraɗiyyar ƙasar nan. Ina kira ga matasan Najeriya su sa ɗan takarar mu a sikelin tantancewa, kana su fito kwansu da kwarkwata su zaɓi ɗan takara mai nagarta a zaɓen 2023."
"Ku zaɓi yan takarar mu tun daga kujerar shugaban ƙasa har ta yan majalisu. Muna kira da ku fito mu haɗa karfi mu kawo canji nagari kuma mu ɗaga Najeriya zuwa babban matsayi, don kawo karshen talauci da wahalhalu a ƙasa."
Meyasa suka zaɓi ficewa daga APC da PDP?
Abu Yanko, wanda ya yi jawabi a wurin a madadin baki ɗaya masu sauya sheƙan. ya shaida wa hukumar dillancin labarai NAN cewa ba su gamsu da tsarukan jam'iyyun PDP da APC ba.
Shugaban LP a Kuje, Oguh Hyginus, ya ce akwai sauran masu sauya sheƙa da ke shirin shigowa jam'iyyar kafin zaɓen 2022l3 domin cigaban demokaraɗiyya a ƙasa.
A wani labarin kuma Gwamnonin babbar jam'iyyar adawa PDP guda huɗu da ke shirin sauya sheƙa sun gana da juna, sun yanke matakin da zasu ɗauka
Gwamna Samuel Ortom na Benuwai ya ce shi da takwarorinsa uku da suka fusata sun yanke cigaba da zama a jam'iyyar PDP.
Gwamna Wike na jihar Ribas, Gwamna Makinde na Oyo da gwamnan Abiya sun ƙauracewa harkokin PDP tun bayan abun da ya faru.
Asali: Legit.ng