Bayan Ganawa a Landan, Gwamnonin PDP Hudu Sun Amince Su cigaba da zama

Bayan Ganawa a Landan, Gwamnonin PDP Hudu Sun Amince Su cigaba da zama

  • Gwamna Samuel Ortom na Benuwai ya ce shi da takwarorinsa uku da suka fusata sun yanke cigaba da zama a jam'iyyar PDP
  • Gwamna Wike na jihar Ribas, Gwamna Makinde na Oyo da gwamnan Abiya sun ƙauracewa harkokin PDP tun bayan abun da ya faru
  • Rikici ya ƙi karewa a babbar jam'iyyar hamayya tun bayan da Atiku ya bayyana zaɓinsa na abokin takara a 2023

Abuja - Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom, ya ce takwaransa na Ribas, Nyesom Wike da sauran gwamnonin PDP da suka fusata da zaɓen abokin takarar Atiku ba zasu bar jam'iyyar ba.

Jaridar Leadership ta rahoto Ortom na cewa Wike da sauran gwamnonin da suka fusata sun amince, bayan ganawa a Landan, cewa suna nan daram a jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku ya bayyana matsayarsa ta yin sulhu da gwamnan PDP Wike

Mataiƙin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, na zaɓen gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin abokin takara ya fusata gwamna Wike da wasu gwamnoni.

Ortom da Wike.
Bayan Ganawa a Landan, Gwamnonin PDP Hudu Sun Amince Su cigaba da zama Hoto: Leadership.ng
Asali: UGC

Gwamna Wike ne ya mamaye zuƙatan jiga-jigan PDP a matsayin wanda ya dace ya zama mataimaki, amma abun ya canza akala daga ƙarshe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wani abu mai kama da zanga-zanga, Wike da wasu gwamnoni da suka haɗa da Seyi Makinde na jihar Oyo, Okezie Ikpeazu, na Abiya sun janye jikin su daga duk wasu harkokin jam'iyya har da zaɓen gwamnan Osun.

Shin dagaske zasu sauya sheƙa daga PDP?

Amma gwamna Ortom na jihar Benuwai, wanda ya bayyana a cikin shirin kafar talabilin ɗin Arise TV, ya bayyana cewa lokacin da yake Landan ya gana da gwamnonin kuma sun yanke zama a PDP.

Kara karanta wannan

Peter Obi ba zai kai labari ba a 2023, kaso 90% na yan arewa basu Soshiyal Midiya, Atiku ya magantu

Ya ce Atiku ya amince ya gana da Wike domin rarrashinsa kan abubuwan da suka faru kuma ya umarci na ja hankalin sa ya amince a yi zaman sulhu.

Gwamnan ya ce:

"Na haɗu da Wike a Landan, na gana da ɗan uwana gwamnan Oyo, Seyi Makinde da gwamnan Abiya, hakan ya bamu damar tattauna wa kan abubuwan da suka faru a jam'iyyar mu ta PDP."
"Abu ɗaya da nake son tabbatar wa yan Najeriya shi ne baki ɗayan mu ba zamu sauya sheƙa daga PDP ba, mu mambobin jam'iyya ne."

A wani labarin kuma Atiku Ya Faɗi Gaskiyar Yadda Alaƙarsa Take da Obasanjo Game da Takara a 2023

Alhaji Atiku Abubakar ya ce ya sa a ransa cewa yana da goyon bayan tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo.

Tun bayan bayyana tsohon mataimakin shugaban a matsayin ɗan takarar PDP, rikici ya ɓarke tsakanin masu ruwa da tsaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel