Shugabar Matan APC ta ƙasa ta tarbi masu sauya sheƙa 20,000 a jihar Cross River

Shugabar Matan APC ta ƙasa ta tarbi masu sauya sheƙa 20,000 a jihar Cross River

  • Shugabar matan APC ta ƙasa, Dakta Betta Enu, ta karɓi dubbannin masu sauya sheƙa zuwa APC a mahaifarta da ke jihar Kuros Riba
  • A wani taro da aka shirya domin tarbar mutanen, Enu ta tabbatar musu da cewa ba za'a nuna musu banbanci ba
  • Manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki reshen jiha da ƙasa sun samu halartar bikin tarban masu sauya shekan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Cross River - A jiya Asabar, kusan mambobi 20,000 na jam'iyyun siyasa suka sanar da sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai a Adadama, ƙaramar hukumar Abi, jihar Kuross Riba, inda ya kasance mahaifar shugabar mata ta ƙasa, Betta Edu.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa ta musamman da aka aike wa jaridar Vanguard a babban birnin tarayya Abuja.

Batte Edu.
Shugabar Matan APC ta ƙasa ta tarbi masu sauya sheƙa 20,000 a jihar Cross River Hoto: Betta Edu/facebook
Asali: Facebook

Rahoto ya nuna cewa an samu wannan guguwar sauyin ne zuwa APC sanadiyyar nasarar da Edu ta samu da kokarinta tun bayan ayyana ta a matsayin shugabaar matan jam'iyya ta ƙasa.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya aike da muhimmin saƙo ga shugaban jam'iyyar APC na ƙasa

Shugaban APC reshen jihar Kuros Riba, Barista Alphonsus Eba, ya roki masu sauya shekan su cigaba da aiki tare da shugabannin su domin su sha romon demokaraɗiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa Allah ya albarkaci jihar da jagora kamar Dakta Betta Edu, inda ya ƙara da cewa rashin sani ne da neman fanɗare wa idan wani ya ƙi yarda su yi aiki a inuwa ɗaya tare da ita.

Barista Eba ya ce:

"Yau ta na da kunnen da za'a saurare ta kuma a maida hankali kanta a gwamnatin tarayya kuma wannan gare mu baki ɗaya wata ƙarin dama ce."
"Mun karɓe ku da zuciya ɗaya zuwa jam'iyyar cigaba a madadin gwamnan mu, Farfesa Ben Ayade kuma muna tabbatar muku a jam'iyyar mu babu sabon zuwa ko tsoho duk ɗaya muke babu banbanci."
"Daga ƙarshe dai Dakta Betta Edu ta rushe baki ɗaya tsarin da aka gina PDP a ƙaramar hukumar Abi domin bana hangen kowa a jam'iyyar."

Kara karanta wannan

Hannun Jari: Najeriya ta samu tsaro daga zuwan Buhari, Minista ya fayyace gaskiya kan abubuwa uku

Zamu baku dama iri ɗaya da kowa - Shugabar mata

A nata ɓangaren, Dakta Betta Edu, ta tabbatar wa masu sauya sheƙan cewa ba za'a nuna musu banbanci ba kuma duk wani shirinta na tallafawa mutane zai cigaba kamar yadda aka san shi.

"PDP ta zama tarihi, ina rokon ku kowa ya tabbata ya yi katin zaɓe domin ya zaɓi jam'iyyar APC tun daga sama har ƙasa. Nan ba da jimawa ba za'a kaɗa gangantar yaƙin neman zaɓe."

Mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Ivara Ejemot Esu, ya halarci wurin taron a madadin gwamna Ben Ayaɗe na jihar Kuros Riba. Haka na wakilan uwar jam'iyya ta ƙasa duk sun halarta.

A wani labarin kuma Gwamnonin PDP huɗu da ke shirin sauyan sheƙa sun gana da juna a Landan, sun yanke shawara ta ƙarshe

Gwamna Samuel Ortom na Benuwai ya ce shi da takwarorinsa uku da suka fusata sun yanke cigaba da zama a jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Haɗin kan ƙasa da tsaron yan Najeriya zan sa a gaba, Buhari ya faɗi abinda zai yi bayan ya sauka mulki

Gwamna Wike na jihar Ribas, Gwamna Makinde na Oyo da gwamnan Abiya sun ƙauracewa harkokin PDP tun bayan abun da ya faru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel