Amaechi: Daliget Da Suka Sayar Da Kuri'unsu Yayin Zaben Fidda Gwani Na APC Suna Nadama

Amaechi: Daliget Da Suka Sayar Da Kuri'unsu Yayin Zaben Fidda Gwani Na APC Suna Nadama

  • Rotimi Amaechi, Ministan Sufuri ya bayyana cewa daliget da suka karbi kudi suka sayar da kuri'unsu yayin zaben fidda gwani na shugaban kasa a APC suna da-na-sani
  • Tsohon gwamnan na Jihar Rivers, wanda shine ya zo na biyu a zaben fidda gwani na shugaban kasa a APC ya bayyana hakan ne a Port Harcourt wurin taro
  • Jigon na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya ce gama-garin yan Najeriya ne matsalar kasar kuma ya kamata su fara gyara kansu ta hanyar zaben wadanda suka cancanta

Rivers - Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri, ya ce daliget din da suka sayar da kuri'unsu a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyar APC suna nadamar abin da suka aikata, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Fitaccen malami: APC faduwa za ta yi a zaben 2023 mai zuwa saboda duk musulmai ne 'yan takarar

Amaechi, tsohon gwamnan Rivers, ya samu kuri'u 316 kuma shine ya zo na biyu a zaben.

Rotimi Amaechi.
Amaechi: Daliget Da Suka Sayar Da Kuri'unsu Yayin Zaben Fidda Gwani Na APC Suna Nadama. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bola Tinubu, tsohon gwamnan Jihar Legas ne ya samu tikitin takarar shugaban kasar bayan samun kuri'u fiye da 1000.

Da ya ke magana wurin taron cika shekaru 60 na Eugene Ogu, shugaban cocin Abundant Life Evangel Mission a Port Harcourt, Amaechi ya ce yan Najeriya ne matsalar kasar.

Amaechi ya ce addu'ar da ya kamata a rika yi shine na zaben wanda ya dace ya jagoranci kasar.

"Ban yarda cewa wannan shine mafita ga matsalolin Najeriya ba- bada kudi. Ina fatan ka sani. Na baka Naira miliyan 10 a yau kuma idan ya kare, me zai faru? Dole kowa ta tashi tsaye kafin a warware matsalar Najeriya," in ji shi.
"Allah ya ceci gamagarin dan Najeriya, domin sune matsalar kasar. Wadanda suka yi zabe a zaben fidda gwani na APC, su wanene? Gamagarin yan Najeriya. Karamin kudin da suka samu ya warware musu matsalarsu na yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya ba Kiristoci Shawara Tun da APC Kinkimo Musulmi da Musulmi a 2023

"Ah, mun yi kuskure; 'ba mu yi kuskure ba'. Muna jin abubuwa daban-daban. Ku yi wa shugabannin kasar nan addu'a, amma ku yi wa gamagarin yan Najeriya addu'a su zabi wanda ya cancanta ya jagorance su."

Mutane Sun Yi Zaton 'Asirin Kudi' Na Ke Yi Saboda Irin Motar Da Na Ke Hawa, Sanatan Najeriya

A wani rahoton, Sanata Orji Kalu, bulaliyar majalisar dattawar Najeriya ya ce wasu yan Najeriya na yada jita-jitan cewa 'asirin kudi' ya ke yi saboda motar da ya ke hawa.

Tsohon gwamnan na Jihar Abia ya ce ba gaskiya bane cewa saboda kudi ya shiga siyasa domin a cewarsa yana kashe kudin aljihunsa don yi wa mutanen yankinsa hidima.

Bulaliyar Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce wasu yan Najeriya sun yi zaton 'yankan kai' ya ke yi saboda zukekiyar mota mai tsada da ya ke hawa a 1982.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164