2023: Ku kwantar da hankali, za fa ku ci zaben nan, Buhari ga Tinubu da Shettima

2023: Ku kwantar da hankali, za fa ku ci zaben nan, Buhari ga Tinubu da Shettima

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kwarin gwiwarsa a zaben 2023, ya ce tabbas Tinubu zai lashe zabe
  • Kashim Shettima ya gana da shugaba Buhari jim kadan bayan kaddamar dashi a matsayin abokin takarar Tinubu
  • Tinubu ya zabi Kashim Shettima a matsayin wanda zai tsaya masa a zaben 2023 mai zuwa, lamarin da ya girgiza Najeriya

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi batu mai ban dariya a fadarsa da ke Abuja yayin da yake martani ga zabo Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu na zaben 2023.

Shugaba Buhari, cikin barkwanci ya ba Tinubu da Shettima kwarin gwiwar lashe zaben shugaban kasa da ke tafe a shekara mai zuwa, Leadership ta ruwaito.

Buhari ya ba Shettima da Tinubu kwarin gwiwa
2023: Ku kwantar da hankali, za fa ku ci zaben nan, Buhari ga Tinubu da Shettima | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Buhari wanda ya karbi bakuncin dan takarar mataimakin shugaban kasa jim kadan bayan shugabannin APC da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu sun kaddamar dashi, ya ce ya yi matukar farin ciki da zabo tsohon gwamnan na jihar Borno.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya yi nadi mai muhimmanci, ya ba wani dan Katsina mukamin babban sakatare

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina yi muku fatan alheri. Tasirin ka a jam'iyyar yana da mutuntawa sosai. Ka yi wa’adi biyu na Gwamna kuma ka gama da lafiya."

Shugaban ya bayyana kwarin gwiwar cewa tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC zai yi nasara a 2023.

Shettima ya godewa Buhari

A nasa jawabin, dan takarar mataimakin shugaban kasar ya godewa shugaban kasar bisa "tausayarwar, goyon baya da kuma rawar da ya taka," wanda ya kai ga fitowarsa takara a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC.

Ya yaba wa shugaban kasa kan samun matsayi na musamman a zukatan jama'ar Borno, yana mai gode masa bisa kokarin da ya yiwa jihar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gida Bai Koshi Ba: Kungiyar Yarbawa Ta Bayyana Wanda Take So Ya Gaje Buhari Tsakanin Obi Da Tinubu

Ya kuma gode masa kan kafa Hukumar Cigaban Arewa maso Gabas (NEDC), da kuma cibiyar samar da wutar lantarki mai zaman kanta na Maiduguri da NNPC ta yi.

Dan takarar APC Tinubu: Dole ne na kwaci Najeriya a 2023 don na samar da ayyukan yi

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya bayyana kadan daga tagomashin da ya tanadarwa 'yan Najeriya, inda ya dage cewa dole ne ya ci zabe.

Bola Ahmad Tinubu, ya magantu ne yayin da yake kaddamar da abokin takararsa Kashim Shettima a babban birnin tarayya Abuja.

Tinubu, ya bayyana cewa, yana da mafarkin kawo sauyi a Najeriya, kuma zai tabbatar da samar da ayyukan yi ga 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.