Atiku Abubakar na cikin koshin lafiya, in ji Mai magana da yawunsa

Atiku Abubakar na cikin koshin lafiya, in ji Mai magana da yawunsa

  • Ana rade-radin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, yana fama da rashin lafiya
  • Kungiyar labaran tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya sun zargi makirai da yada jita-jitan rashin lafiyan Atiku
  • Hadimin Atiku, Mazi Paul Ibe, ya jadadda cewar ubangidansa na cikin koshin lafiya kuma babu abun da ya same shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kwamitin masu yada muradun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, sun yi watsi da jita-jitan da ake yadawa game da lafiyarsa, jaridar Vanguard ta rahoto.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai ba tsohon mataimakin shugaban kasar shawara kan harkokin labarai, Mazi Paul Ibe.

Kwamitin ta ce ta ga ya dace ne ta yi gyara ga wani rahoto da bidiyo da wasu makirai suka fitar inda suka nuna Atiku Abubakar cikin wani hali na rashin lafiya harma wani hadiminsa na taimaka masa wajen gyara zama a mota.

Kara karanta wannan

2023: APC, PDP Na Fuskantar Babban Barazana A Yayin Da Peter Obi Ya Fara Kamfen A Arewa, Ya Ziyarci Dattijon Arewa Mai Karfin Fada A Ji

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar na cikin koshin lafiya, in ji kungiyar labaransa Hoto: punchng.com
Asali: Facebook

Ibe ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Babu wani abu da zai wuce gaskiya. Ku sani, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yana ciki koshin lafiya.
“Da haka kawai ne ba za mu yi martani kan wannan makircin ba, amma mun yi martani ne saboda abun da hakan zai haddasa a zukatan yan Najeriya, wanda dama shine manufar watsa wannan labarin karyan.
“Ku tuna cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa na PDP ya kasance a Osogbo, babban birnin jihar Osun a ranar Alhamis don gangamin PDP, gabannin zaben gwamna da aka yi a karshen makon jiya wanda dan takarar jam’iyyar, Sanata Ademola Adeleke ya yi nasara.
“Yana da muhimmanci a sani cewa an tanadi duk wasu matakan kariya don tabbatar da tsaron lafiya da duk wani motsi na babban mutum.

Kara karanta wannan

Shettima: Yan Najeriya Sun Tattare Kan Addini Yayin Da Sauran Kasashe Ke Kara Azama a Bangaren Fasaha

“Hakkin shugaban masu tsaron Atiku Abubakar ne ya tabbatar da tsaron lafiyarsa kafin ayarin motocin su fara kowani irin tafiya. Tunda tafiyar manya ya kunshi tukin kariya, tabbatar da tsaron babban mutum kafin a fara kowani irin tafiya mai nisa ko mara nisa. Babban abun da ake la’akari da shi a koda yaushe shine tsaron lafiyar Atiku."

Mista Ibe ya ce Atiku bai kyamaci a tantance shi ba saboda yanayin zaben 2023, jaridar Premium Times ta rahoto.

Atiku Ya Taya Adeleke Murnar Lashen Zaben Gwamnan Jihar Osun

A wani labarin, mun ji a baya cewa tsohon Mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a Jami’yyar People’s Democratic Party PDP Alhaji Atiku Abubakar, ya taya Ademola Adeleke murnar lashe zaben gwamnan jihar Osu.

Rahoton Legit.NG A ranar Asabar ne aka gudanar da zaben gwamnan cike da tsauraran matakan tsaro.

Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana farin cikin sa ne a shafin sa na Tuwita inda yace :

Kara karanta wannan

Jita-jitar barin APC: Hadimin Farfesa Yemi Osinbajo ya fito, ya fadi gaskiyar lamari

“Haske ya shigo jihar Osun, ina taya Jam’iyyar PDP da masu ruwa da tsaki murnar wannan nasarar da aka samu.
“Ina kuma taya alummar Jihar Osun da suka tabbatar wa duniya ce wa, tabbas mulki yana hannun al’umma ne."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng