Atiku Ya Taya Adeleke Murnar Lashen Zaben Gwamnan Jihar Osun

Atiku Ya Taya Adeleke Murnar Lashen Zaben Gwamnan Jihar Osun

  • Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya taya Ademola Adeleke murnar lashe zaben gwamnan jihar Osun
  • Alhaji Atiku Abubakar ya ce nasarar Ademola Adeleke a zaben jihar Osun ya nuna mulki a hannun al'umma yake
  • Sanata Adeleke ya samu kuri’a 403,371 gwamna Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC ya zo na biyu da kuri’a 375,027

Jihar Osun - Tsohon Mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a Jami’yyar People’s Democratic Party PDP Alhaji Atiku Abubakar, ya taya Ademola Adeleke murnar lashe zaben gwamnan jihar Osu. Rahoton Legit.NG

A ranar Asabar ne aka gudanar da zaben gwamnan cike da tsauraran matakan tsaro.

Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana farin cikin sa ne a shafin sa na Tuwita inda yace :

atiku
Atiku Ya Taya Isiaka Adeleke Murnar Lashen Zaben Gwamnan Jihar Osun : FOTO Twitter
Asali: Facebook
“Haske ya shigo jihar Osun, ina taya Jam’iyyar PDP da masu ruwa da tsaki murnar wannan nasarar da aka samu.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya lashe zaben gwamnan jihar Osun

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Ina kuma taya alummar Jihar Osun da suka tabbatar wa duniya ce wa, tabbas mulki yana hannun al’umma ne.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP),Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.

Dan takarar na PDP ya lashe kananan hukumomi 17 yayin da gwamna Gboye Oyetoa ci kananan hukumomi 13. Rahoton jaridar PUNCH.

Adeleke ya samu kuri’u 403, 371 inda lallasa babban abokin hamayyarsa gwamna Gboyega Oyetola na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), da ya samu kuri’u 375,027.

Zaben gwamnan Osun: Abubuwa 7 masu muhimmanci game da dan takarar da ya kawo karshen APC

A wani labari kuma, Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP ne ya lashe zaben kamar yadda rahotanni suka bayyana da sanyin safiyar yau Lahad 17 ga watan Yulin 2022.

To amma, meye kuka sani game da wannan dan takara na gwamna ya lashe zaben, kuma ya kawo karshen mulkin jam'iyyar APC mai ci?

Asali: Legit.ng

Online view pixel