2023: Yan majalisar dokoki 192 na shirin ficewa daga APC, In ji kwamitin Babachir
- Rahotanni sun kawo cewa 'ya'yan APC 192 a majalisar dokokin tarayya sun shirya tsaf don ficewa daga jam'iyyar
- Hakan ya biyo bayan rasa tikitin komawa kan kujerunsu da suka yi a zaben fidda gwanin jam'iyyar mai mulki
- Kwamitin Babachir David ne ya bayyana hakan a rahotonsa inda ya yi kira ga Buhari da manyan jiga-jigan jam'iyyar da su shigo lamarin
Kwamitin tsare-tsare da dabaru na kungiyar kamfen din Tinubu ta bayyana cewa akalla mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a majalisar dokokin tarayya 192 suna shirin sauya sheka daga jam’iyyar sakamakon zaben fidda gwanin jam’iyyar da yasa wasun su suka rasa tikitin komawa majalisa.
Kwamitin karkashin jagorancin tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawan, ya bayyana haka a cikin rahoton tabbatar da shugabancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023 mai zuwa.
Shettima: Yan Najeriya Sun Tattare Kan Addini Yayin Da Sauran Kasashe Ke Kara Azama a Bangaren Fasaha
Kwamitin wanda ya lissafa abubuwan da ya kamata jam’iyyar ta yi la’akari da su wajen tsayar da abokin takara ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, shugabannin majalisar dokokin kasar da sauran shugabannin jam’iyyar da su shiga lamarin.
Jaridar Punch ta rahoto cewa kwamitin ya kuma yi gargadin cewa sauya shekar yan majalisar na iya zama karan tsaye ga jam’iyyar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoton kwamitin na da mambobi 23, wanda 22 daga cikinsu suka sanyawa takardar hannu illa tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Nuhu Ribadu, da bai saka hannu ba.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara; sanatoci masu ci Opeyemi Bamidele, Ishaku Abbo, Grace Bent da Basiru Ajibola; yan majalisar wakilai Musa Sarkin-Adar, Komsol Longgap da Olawale Raji; tsoffin sanatoci Adesoji Akanbi, Abu Ibrahim da Magnus Abe.
Sauran sune Darakta Janar na kungiyar goyon bayan Tinubu, Umar Mohammed; mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Silas Agara; tsohon mataimakin gwamnan jihar Lagas, Femi Pedro; Safaa Adam; Amina Indala; Kashim Imam; Akin Awodeyi-Akinseyiwa; Saadatu Garba; Abubakar Sanusi da M.T Usman.
Rahoton kwamitin wanda aka ce an mikawa Tinubu don dubawa da aiwatar da shi ya ce:
“Sauya sheka zuwa wasu jam’iyyu ba sabon abu bane a lokacin zabe amma ya zo da damuwa a wannan zaben domin manyan mambobi da dama sun fusata da tsarin zaben.
“Akwai bukatar a tuntubi manyan jami’an majalisar dokokin tarayya da shugabannin jham’iyyar a matsakin tarayya, jiha, yanki da kananan hukumomi domin tausar mutanen da suka fusata.
“Abun damuwa ne cewa sanatoci masu ci 22 da mambobin majalisar wakilai 170 suna shirin sauya sheka daga APC. Babu shakka wannan zai raunana karfinmu kuma akwai bukatar shugaban kasa, dan takararmu na shugaban kasa, gwamnoni, shugabannin majalisar dokoki, shugabannin APC na kasa, jiha, yanki da kananan hukuma da manyan masu fada aji a jam’iyyar su saka baki a lamarin.”
Punch ya kuma rahoto cewa kwamitin ya gana sau da dama a watan Yuli kuma ya tattauna lamuran abokin takara, tare da la’akari da addini; suna da kuma nagartar dan takara; sauya shekar mambobin jam’iyyar da kuma daidaiton jinsi.
Game da batun abokin takara, kwamitin ya yi nuni da cewa, tikitin takarar musulmi da musulmi da kuma musulmi da kirista na da fa'ida da rashin fa'ida, sai dai ya yi gargadin cewa yanki da addinin abokin takara wasu batutuwa ne masu muhimmanci da ke bukatar yin nazari sosai.
Yanzu Yanzu: Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya lashe zaben gwamnan jihar Osun
A wani labari na daban, mun ji cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP),Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.
Baturen zabe a jihar, Toyin Ogundipe, ne ya sanar da sakamakon zaben a safiyar ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, jaridar The Cable ta rahoto.
Adeleke ya samu kuri’u 403, 371 wajen lallasa babban abokin hamayyarsa Gboyega Oyetola na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ya samu kuri’u 375,027.
Asali: Legit.ng