Ganduje ga Musulman Osun: Ku zabo Oyetola saboda shi Musulmi ne

Ganduje ga Musulman Osun: Ku zabo Oyetola saboda shi Musulmi ne

  • Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano ya bukaci Musulman Osun da su zabi dan takarar APC, Gboyega Oyetola, a karo na biyu saboda shi Musulmi ne
  • Ganduje ya bayyana hakan yayin da ya ziyarci wani Masallacin Juma'a a jihar ta Osun inda ya zanta da al'ummar Hausawa
  • Ya kuma bayyana cewa an shawarci Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar mai mulki da ya zabi Musulmi kuma ya bi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Osun - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya bukaci daukacin al’umman Musulmai a jihar Osun da su zabi gwamna mai ci, Gboyega Oyetola, don ya ci gaba da mulki a matsayin gwamna karo na biyu saboda shi Musulmi ne kamar su.

Ya bayyana cewa Oyetola ne gwamna Musulmi daya tilo a kudu maso yamma, yana mai cewa shi din dan uwansu ne.

Kara karanta wannan

2023: Tikitin Musulmi Da Kirista Da Muka Yi A Baya Bai Tsinana Mana Komai Ba, Oshiomhole

Ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan murya da sashin Hausa na BBC ya saki a daren ranar Juma’a.

Gwamnan jihar Osun a Masallaci
Ganduje ga Musulman Osun: Ku zabo Oyetola saboda shi Musulmi ne Hoto: hallmarknews.com
Asali: UGC

Jaridar Punch ta rahoto cewa Ganduje ya ziyarci masallaci a Osogbo a ranar Juma’a a yayin sallar Juma’a, inda ya gana da al’ummar Hausawa a Osogbo, don nemawa Oyetola kuri’u.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ganduje ya ce:

“Na zo masallaci don zantawa da Musulman da ke nan. Dan Allah, mutumin da za ku zaba shine Oyetola. Kun san dalili? Saboda shi Musulmi ne kamar ku. Muna jagorantarku kan hanyar da za ku bi.”

Ganduje ya kuma bayyana cewa an bukaci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya zabi Musulmi a matsayin abokin takara, inda ya aikata hakan.

A cewarsa, wannan ya isa dalili da zai sa su zabi gwamna mai ci, wanda ya yi ikirarin zai gina kasuwanni, hanyoyi da kuma kawo ci gaba a cikin al’ummarsu.

Kara karanta wannan

Zaben Osun : Ba Aikinmu Bane mu hana saye da Siyar da Kuri'u, Inji Kwamishinan INEC

Da yake amsa wata tambaya da jama’a suka tambaye shi sai ya ce:

“Don ci gaban kasar nan, bai kamata mu zama masu son kai na addini ba.
“Kiristoci suma yan uwanmu ne. ya zama dole mu mara masu baya.
“Lokacin da Hausawa suka ce sune ya kamata su dawo kan kujerar, muka ce a’a, zagayen Yarbawa ne.
“Wannan dalilin ne yasa muka zabi Bola Ahmed Tinubu. Wannan ne hanya daya da za mu bi don hana fada da rikici. Ina a nan ne don taimakawa dan uwanmu (Oyetola) wanda muke so ya lashe zabe.”

Shettima: Yan Najeriya Sun Mayar Da Hankali Kan Addini Yayin Da Sauran Kasashe Na Bunkasa Ta Fasaha

A wani labarin kuma, Sanata Kashim Shettima, abokin takarar Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023 ya ce su dena takaita tunaninsu kan addini yayin zaben shugabanni, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya ci zabe ya gama, In ji tsohon dan takarar kujerar gwamna a Plateau

Zaben Shettima da a matsayin mataimakin Tinubu ya janyo suka daga mutane saboda su biyu musulmi ne.

Da ya ke magana a ranar Juma'a yayin da ya karbi bakuncin tawagar APC karkashin jagorancin Mohammed Hassan, tsohon jakadan Najeriya a Amurka, tsohon gwamnan na Borno ya ce abin da ke gabansa da Tinubu shine sauya kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng