2023: Jerin sunayen yan takarar mataimakin shugaban kasa 10 da kwamitin APC ya gabatarwa Tinubu

2023: Jerin sunayen yan takarar mataimakin shugaban kasa 10 da kwamitin APC ya gabatarwa Tinubu

  • Bayanai da ke fitowa sun tabbatar da cewar akwai sunayen wasu mutane da aka gabatarwa Tinubu domin ya zabi mataimakin shugaban kasa a cikinsu
  • Wani rahoto ya nuna cewa takardar da aka gabatarwa dan takarar shugaban kasar na dauke da sunayen mutane goma kuma babu sunan Sanata Kashim Shettima a ciki
  • An tattaro cewa wani kwamiti karkashin jagorancin tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ne suka gabatar da sunayen

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kafin bayyana Sanata Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC mai mulki, an kafa wani kwamiti don ba wanda ke rike da tutar jam'iyyar, Bola Ahmed Tinubu shawara kan wanda zai tsayar a matsayin abokin takara.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto a ranar Alhamis, 14 ga watan Yuli, kwamitin ya gabatarwa Tinubu da sunayen yan takara 10.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Kada ku yarda wani fasto ko limami ya fada maku wanda za ku zaba, Keyamo ga yan Najeriya

Tinubu
2023: Jerin sunayen yan takarar mataimakin shugaban kasa 10 da kwamitin APC ya gabatarwa Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa sunan Shettima baya cikin jerin sunayen da kwamitin na APC ya gabatar.

Kamar Atiku Abubakar na Peoples Democratic Party (PDP) Tinubu ma ya yi watsi da shawarar da kwamiti ya basa inda ya dauki Sanata Shettima ya kuma bayyana shi a matsayin abokin takararsa a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, Tinubu ya gabatar da Shettima ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin da ya kai masa ziyarar ban girma a gidansa da ke Daura, jihar Katsina.

Lawal ya gabatarwa Tinubu da sunayen a Landan

Majiyar ta ce an kammala hada rahoton a ranar Talata, 5 ga watan Yuli sannan Lawal ya gabatar da shi a gaban Bola Tinubu a Landan washegarin ranar.

Wani mamba na kwamitin wanda ya tabbatar da hakan ya kuma bayyana cewa tuni aka aikawa Tinubu da kwafin sunayen ta yanar gizo kafin Lawal ya gabatar masa da rubutaciyyar takardar.

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi Da Musulmi Kaddara Ce Daga Allah, Shugaban APC, Adamu

Ga jerin sunayen yan takarar da aka gabatar don zama mataimakin shugaban kasa kamar yadda Daily Trust ta rahoto:

1. Yakubu Dogara (tsohon kakakin majalisar wakilai)

2. Amina J. Mohammed (Mataimakiyar babban sakataren majalisar dinkin duniya)

3. Ambasada Fatima Balla

4. Sanata Anthony Manzo

5. Hajiya Najatu Mohammed

6. Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko

7. Babagana Zulum (gwamnan jihar Borno)

8.Nasir El-Rufai (gwamnan jihar Kaduna)

9. Atiku Bagudu (gwamnan jihar Kebbi)

10. Kashim Imam.

2023: Tinubu ya ci zabe ya gama, In ji tsohon dan takarar kujerar gwamna a Plateau

A wani labarin, mun ji cewa tsohon dan takarar gwamnan jihar Plateau karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), David Victor Dimka, ya yi hasashen cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu ne zai lashe zaben 2023.

Dimka, wanda ya kasance tsohon kwanturolan hukumar kwastam a wata hira da manema labarai a garin Jos, ya ce Tinubu dan siyasa ne da ya yarda da hadin kai da ci gaban Najeriya a matsayin kasa daya, Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Na sanyawa Tinubu da Shettima albarka, in ji Ali Modu Sheriff

Ya bayyana cewa duba ga tarin nasarorinsa a siyasa, Tinubu mutum ne wanda ke da abun da ake bukata don inganta Najeriya, duba da irin ci gaban da ya samu wanda a cewarsa ya shafi dukkan bangarorin rayuwa a fadin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng