Daga komawa Jam’iyyar APC, Orubebe ya samu mukami mai tsoka a zaben 2023
Sanata Ovie Omo-Agege ya zabi Godsday Elder Orubebe ya jagoranci yakin neman zabensa a APC
Mataimakin shugaban majalisar dattawan na Najeriya yana takarar kujerar Gwamnan jihar Delta
Ima Niboro ya bada sanarwar nada Orubebe wanda bai dade da barin PDP zuwa jam’iyyar APC ba
Delta - Ovie Omo-Agege ya bada sanarwar nada Godsday Elder Orubebe a matsayin Darekta Janar na kwamitin yakin neman zaben gwamnansa a jihar Delta.
Rahoton da Channels TV ta fitar a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli 2022, yace Ovie Omo-Agege ya zabi Godsday Elder Orubebe ya zama jagoran kamfe dinsa.
Sanata Ovie Omo-Agege wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar dattawa na kasa a Najeriya, yana neman kujerar gwamnan Delta a jam’iyyar APC a 2023.
A wata sanarwa da ‘dan takaran ya bada ta bakin Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zabensa, Ima Niboro, ya ce an dauko Godsday Elder Orubebe.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Orubebe ya san kan aiki - Kwamiti
Ima Niboro a jawabin da ya fitar a jiya, ya bayyana cewa dalilin dauko tsohon Ministan harkokin Neja-Delta na kasar ya jagoranci yakin zaben shi ne ya san aiki.
“Orubebe tare da ni, za mu jagoranci muhimman zama da tattaunawa da za ayi, saboda kuma kwarewarsa a jam’iyyar adawa ta PDP.”
“Tare da sauran ‘yan kwamiti, za mu yi waje da PDP daga gidan gwamnati a ranar 29 ga watan Mayun 2023, kawo shi zai karfafi tafiyar.”
- Ima Niboro
Sanarwar ta ce Godsday Orubebe za isa APC ta shiga lungu da sako domin yakin neman zabe.
APC ta ci riba da Orubebe
Leadership ta rahoto kwamitin neman takaran Omo Agege yana nuna farin cikin yadda ‘dan siyasar ya fice daga jam’iyyar PDP, ya zabi ya shigo APC mai mulki.
Sanarwar ta ce baya ga matsayin Ministan tarayya sau biyu, Orubebe ya rike Kansila da shugaban karamar hukuma, sannan ya yi shugaban jam’iyya a matakin jiha.
Ganin ya rike mukamai a gwamnatin tarayya da jiha, kwamitin neman zaben yake cewa takarar APC za ta amfana sosai da Orubebe a takarar gwamnan da za ayi.
Babu zaman lafiya a Ribas
A jihar Ribas, an samu rahoto APC ta gamu da cikas domin rigimar Sanata Magnus Abe da tsohon Ministan Tarayya watau Rotimi Amaechi ba ta zo karshe ba
Sanata Abe ya ce ba zai goyi bayan wanda jam’iyyar APC ta ba takara ba domin yana ganin babu gudumuwar da Tony Cole ya taba ba AP
Asali: Legit.ng