Mun daina bacci har sai Tinubu da Shettima sun gaje Buhari, Matasan APC a arewa

Mun daina bacci har sai Tinubu da Shettima sun gaje Buhari, Matasan APC a arewa

  • Gabannin zaben shugaban kasa na 2023, tikitin Tinubu/Shettima na sake samun goyon baya musamman a arewacin kasar
  • Kungiyar matasan APC a arewa ta jinjinawa wannan hadi inda ta sha alwashin jajircewa har sai ta ga Tinubu ya dare kujerar Buhari
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kiristocin yankin arewacin kasar ke ganin ba a kyauta masu ba da tikitin Musulmi da Musulmi

Kungiyar matasan APC a arewa ta jinjinawa dan takarar shugaban kasa na APC da manyan jiga-jigan jam’iyyar kan zabar Sanata Kashim Shettima a matsayin wanda zai daga tutar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.

Shugaban kungiyar Hon. Suleiman Liba ya bayyana cewa ba za su yi bacci ba har sai sun ga Tinubu da Shettima sun yi nasara a babban zaben mai zuwa, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rabiu Kwankwaso Ya Yi Alkawarin Maida WAEC, NECO, JAMB Kyauta Idan Ya Gaji Buhari

Tinubu da Shettima
Mun daina bacci har sai Tinubu da Shettima sun gaje Buhari, Matasan APC a arewa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da yake zantawa da manema labarai, Liba ya ce:

“Wannan zabi shine mafi dacewa ga jam’iyyar kuma shine tsarin lashe zaben 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Shettima kwararren dan siyasa ne wanda ya kafa dimbin tarihi.”

Hon. Liba ya ce ya kamata yan Najeriya musamman mambobin jam’iyyar adawa su daina rura wutar fitina a siyasa ta hanyar cewa tikitin Musulmi da Musulmi na APC ba shine mafita ba.

A cewarsa, ba akidar addini yan Najeriya za su zaba ba face cancanta da nagarta wanda daga Tinubu har Shettima suna da ita.

Jaridar ta nakalto Liba na ci gaba da cewa:

“Lokaci ya yi da za a yi aiki yadda ya kamata don tabbatar da nasarar wannan aiki a zaben 2023.
“Tuni muka fara aiki, domin mun rigada mun buga fastoci dauke da hotunan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima, wanda za a watsa su a fadin jihohin arewa 19 da babbar birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Shettima Ya Magantu Kan Tattaunawa da Kwankwaso Ya Koma Bayan Tinubu a Zaben 2023

“Muna da karfin gwiwar cewa APC za ta yi nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa, amma kuma ba za mu yi bacci ba kuma dole mu hada hannu don tabbatar da nasarar APC a 2023.
“Baya ga watsa fastocin, kungiyar ta kammala tsare-tsare don gudanar da gagarumin gangami a fadin arewa don wayar da kan jama’a kan yin rijistan zabe har a cikin kauyuka.
“Muna alfahari da tsarin nan kuma za mu yi aiki ba ji ba gani don tabbatar da ganin mafarkinmu ya zama gaskiya.”

Ba za mu sake yiwa Tinubu kamfen ba saboda zabar Musulmi da ya yi, Kiristocin APC a arewa

Agefe guda, shugabannin kiristoci na APC a arewa sun bayyana cewa ba za su iya yiwa jam’iyyar kamfen ba saboda tsayar da Musulmi da Musulmi da aka yi a matsayin yan takara shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa. Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Obi ko Atiku? Bincike Ya Nuna Wanda Zai Ci Zaɓen Shugaban Ƙasa, An Bayyana Abin Da Zai Faru

A ranar Lahadi ne dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, ya bayyana Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa na zaben 2023. Hakan ya haifar da cace-kuce daga kungiyoyi daban-daban a fadin kasar nan.

A cikin wata takarda da suka saki bayan wani taro a ranar Litinin, shugabannin Kirista a fadin jihohin arewa 19 sun yi bore kan tikitin Musulmi da Musulmi na APC. Wasu ‘ya’yan jam’iyyar ma sun yi murabus kan wannan al’amari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng