Abin da Shehu Sani ya sani game da alakar Abokin takarar Tinubu da Boko Haram

Abin da Shehu Sani ya sani game da alakar Abokin takarar Tinubu da Boko Haram

  • Shehu Sani ya shiga maganar zargin da ake yi wa Kashim Shettima na alaka da ‘Yan Boko Haram
  • Tsohon ‘Dan Majalisar ya bayyana cewa tsohon Gwamnan na Borno bai da alaka da ‘Yan ta’adda
  • Bugu da kari, Sanata Shehu Sani ya bayyana irin kokarin da Gwamnatin Shettima ta yi a Borno

Kaduna - Legit.ng ta ce Shehu Sani wanda ya yi kaurin suna a fafutuka da gwagwarmaya, ya tofa albarkacin bakinsa game da takarar shugaban kasa.

Sanata Shehu Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya soki zargin da ake yi wa Sanata Kashim Shettima na alaka da ‘Yan Boko Haram.

Da yake magana a wani jawabi da ya fitar a ranar Litinin, 11 ga watan Yuli 2022, Shehu Sani ya nuna ba daidai ba ne a jefi Shettima da wannan mugun zargi.

Kara karanta wannan

Babban Lauyan Najeriya ya raba gardama game da takarar Musulmi da Musulmi a APC

Sanatan yake cewa babu laifi idan wasu sun nuna fushinsu a game da yadda APC ta yi watsi da Kiristoci, ta tsaida Musulmi da Musulmi a babban zaben Najeriya.

Babu adalci a zargin da ake yi

Amma ‘dan siyasar yana ganin wuce gona da iri ne a jefi Kashim Shettima da wata alaka da ‘Yan ta’addan da ya taimaka sosai wajen ganin bayansu a Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Shettima shi ne Gwamna a lokacin da rikicin Boko Haram ya yi kamari a Arewa maso gabas, yanzu ya zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Kashim Shettima
Sanata Kashim Shettima Hoto: bornosocialmedia
Asali: Facebook

“Shettima da yake Gwamnan Borno ya batar da lokacinsa, karfinsa da dukiyar jihar Borno sosai wajen yaki da fito-na-fito da magance matsalar ‘yan ta’addan.”
“Shettima bai da hannu wajen dauke ‘Yan matan Chibok. Ya fi kowa kokari wajen taimakawa aikin sojoji da jami’an tsaro wajen kare Borno da kasa.”

Kara karanta wannan

Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari ya fito yana adawa da takarar Musulmi-Musulmi

- Shehu Sani

Sani yake cewa a matsayin mai ruwa da tsaki, kuma tsohon shugaban kwamiti majalisar dattawa a kan rikicin Arewa maso gabas, ya san irin kokarin Shettima.

A rahoton This Day, an ji tsohon ‘dan majalisar yana mai cewa Shettima ya kawo kungiyoyi masu zaman kansu watau NGOs da kasashe domin su taimakawa yankin.

Shettima ya cancanta – Shehu Sani

Duk da shi ba ‘Dan APC ba ne kamar yadda ya fada, Shehu Sani ya ce maganar gaskiya Shettima ya fi sauran wadanda ake tunanin za a ba tikitin cancanta.

Mutane ba su dauki addini da wasa a Najeriya ba, amma duk da haka, tsohon Sanatan yana ganin Najeriya za ta amfana da kwarewar Shettima a harkar tsaro.

Tony Princewill ya bar APC

A jiya an labari Tony Princewill ya yi fushi da Bola Tinubu ya yi fatali kiristocin da ke Arewacin Najeriya, ya dauko Musulmi a matsayin abokin takararsa a zaben 2023.

Kara karanta wannan

2023: Ministan Buhari ya jero abubuwan da ke nuna cancantar takarar Shettima

Tony Princewill ya ce ba zai iya kare APC ba, don haka ya bada sanarwar barin jam'iyya, har kuma ya yi kira ga mai gidansa, Rotimi Amaechi da ya biyi sahunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel