Mataimakin shugaban kasa: Jiga-jigan APC a arewa maso gabas sun jinjinawa APC da Tinubu kan zabar Shettima

Mataimakin shugaban kasa: Jiga-jigan APC a arewa maso gabas sun jinjinawa APC da Tinubu kan zabar Shettima

  • Jiga-jigan APC a arewa maso gabas sun jinjinawa APC da Tinubu kan zabar Kashim Shettima da suka yi a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa
  • A ranar Lahadi ne Tinubu ya bayyana tsohon gwamnan na jihar Borno a matsayin abokin takararsa na zaben shugaban kasa na 2023
  • Shugaban majalisar dattawa, Lawan Ahmad, ya ce Shettima ya cancanci zama mataimakin shugaban kasar Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Dr Ahmad Lawan, da manyan jiga-jigan APC a arewa maso gabas sun taya Sanata Kashim Shettima murnar zabarsa da aka yi a matsayin mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023.

Shettima shine abokin takarar Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki.

Lawan, a wata sanarwa da ya fitar a madadin jiga-jigan yankin a Abuja a ranar Litinin, 11 ga watan Yuli, ya ce Tinubu da APC sun yi zabi mai kyau a Shettima, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tikitin Tinubu da Shettima mabudin nasara ne ga jam'iyyar APC, gwamna Buni

Shettima da Tinubu
Mataimakin shugaban kasa: Jiga-jigan APC a arewa maso gabas sun jinjinawa APC da Tinubu kan zabar Shettima Hoto: @HoeGee_Tyla
Asali: Twitter

A cewar Lawan, Shettima wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Borno sau biyu, ya shiga aikin gwamnati da takardu masu kyau, wanda ya samu ci gaba ta hanyar nuna kwarewa, rikon amana da jajircewa a dukkan mukaman da ya rike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lawan ya ce tarin ilimin Shettima da aikin da ya yi a kamfanoni masu zaman kansu sun taka rawar gani a nasarorin da ya samu a matsayin gwamna da sanata.

Ya ce dan takarar mataimakin shugaban kasar na APC ya kasance mutum mai biyayya kuma jajirtaccen dan jam’iyyar, inda ya kara da cewa yana da abubuwan bukata don zama mataimakin shugaban kasar Najeriya.

Daily Post ta nakalto Lawan yana cewa:

“Mu, jiga-jigan APC a arewa maso gabas mun tabbatar da cewar Shettima shine mutumin da ya dace da aikin kuma zai kasance mai biyayya ga Tinubu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan ganawa da Buhari, gwamnonin APC sun fadi matsayarsu kan takarar Tinubu da Shettima

“A matsayinmu na jiga-jigai, mun yi alkawarin bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga yan takararmu don cimma nasara a babban zaben.
“Muna umartan dukkanin mambobin jam’iyyarmu a fadin Najeriya da su ba dan takarar APC da abokin takararsa cikakken goyon bayansu.
“Mun kuma ba yan Najeriya tabbacin cewa zabin da jam’iyyarmu ta yi na tikitin shugaban kasarmu shine mafi kyau a kasarmu.”

2023: Ministan Buhari ya jero abubuwan da ke nuna cancantar takarar Shettima

A gefe guda, karamin Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasa, Festus Keyamo (SAN), yana cikin wadanda suka yabi zabin Kashim Shettima.

Festus Keyamo (SAN) ya yi magana a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli 2022, yana mai cewa Kashim Shettima ya dace da takara.

Sanata Kashim Shettima shi ne wanda ‘dan takaran kujeran shugaban kas ana APC watau Bola Ahmed Tinubu ya dauko a matsayin abokin takara.

Kara karanta wannan

Naka sai naka: Shugaban kungiyar CAN a Borno ya goyi bayan takarar Shettima

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng