Yanzun nan: An yi ram da daya daga cikin wadanda suka tsere daga kurkukun Kuje
- Jami’an hukumar NDLEA masu yaki da miyagun kwayoyi sun bada sanarwar kama Suleiman Idi
- Suleiman Idi yana cikin ‘yan ta’addan da suka sulale daga gidan gyaran halin Kuje a makon da ya wuce
- Kamar yadda rahoto ya nuna, an cafke ‘Dan ta’addan ne yana shirin hawa mota zuwa Maiduguri
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja – Rahotanni na zuwa cewa daya daga cikin ‘yan ta’addan da suka tsere daga gidan gyara hali na Kuje a birnin tarayya ya fada hannun jami’ai.
Daily Trust ta fitar da rahoto dazu cewa karyar daya daga cikin miyagun ta kare ya shiga hannun hukuma.
A ranar Litinin, 11 ga watan Yuli 2022, jami’an hukumar NDLEA masu yaki da miyagun kwayoyi suka yi nasarar damke Suleiman Idi a tashar mota.
Rahoton yake cewa ma’aikatan na NDLEA sun kama Suleiman Idi a tashar motoci da ke unguwar Area I a babban birnin tarayya Abuja, yana neman sulalewa.
Mai magana da yawun bakin NDLEA na kasa, Femi Babafemi ya bayyana cewa an kama Idi ne yana yunkurin shiga mota zuwa Maiduguri a jihar Borno.
“Da aka soma yin bincike, ‘dan ta’addan da ake zargi ya tabbatar da cewa yana cikin wadanda aka tsare a gidan gyaran hali na Kuje.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Idi ya tabbatar da an tsare shi ne bisa zargin ta’addan da fashi da makamai, ya bayyana yana cikin wadanda suka tsere a ranar Talata.
Baya ga haka, ma’aikatan na NDLEA sun samu moli uku na tabar wiwi a jikin Suleiman Idi.
- Hukumar NDLEA
An fasa gidan yarin Kuje
‘Yan ta’addan Islamic State West Africa Province (ISWAP) sun tabbatar da su ke da hannu a wajen wannan ta’adi da aka yi, aka tsere da ‘Yan Boko Haram.
Hukumar gyaran hali na kasa, Nigerian Correctional Service (NCoS) ta fitar da jerin sunaye da hotunan ‘yan ta’addan da suka kubuta daga gidan gyaran halin.
Mutum biyu sun shiga hannu
Wannan shi ne mutum na biyu da aka cafke bayan ‘yan ta’adan sun fasa gidan gyaran halin na Kuje, inda suka yi nasarar kubutar da sama da mutane 800.
A baya ‘yan sanda na jihar Nasara sun bada sanarwar cafke wani Hassan Hassan. Kwamishinan ‘yan sanda, Adesina Soyemi ya bada umarni a garkame shi.
Asali: Legit.ng