Tikitin Musulmi da Musulmi: Kungiyar arewa ta jero abubuwa 3 da Tinubu zai fuskanta
- Ana ci gaba da takaddama kan zabin Bola Tinubu na daukar Musulmi a matsayin abokin takararsa a zaben 2023 mai zuwa
- Kakakin kungiyar dattawan arewa ya bayyana cewa babu abun da wannan zabi na Tinubu zai sauya a makomar siyasarsa
- Tsohon gwamnan na jihar Lagas dai ya tsayar da Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a babban zaben kasar
Kungiyar dattawan arewa ta yi martani a kan zabar Musulmi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya yi domin ya zama abokin takararsa a 2023.
NEF ta lissafa wasu abubuwa guda uku da za su faru ga Tinubu a yanzu da ya zabi yin tikitin Musulmi da Musulmi a babban zaben kasar mai zuwa.
Kakakin kungiyar dattawan arewan, Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa wannan mataki da Tinubu ya dauka ba zai kawo kowani sauyi a makomar zabensa ba.
A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, 11 ga watan Yuli, Baba-Ahmed ya lissafa abubuwa uku da ka iya faruwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
- Kiristoci za su juyawa tikitin baya.
- Daukacin al’ummar Musulmi za su marawa wannan tikiti nasa baya.
- Babu wani sauyi da hakan zai kawo ga makomar zabensa.
Naka sai naka: Shugaban kungiyar CAN a Borno ya goyi bayan takarar Shettima
A wani labarin kuma, shugaban kungiyar kiristocin Najeriya reshen jihar Borno, Bishop Mohammed Naga, ya yaba da zabar tsohon gwamnan jihar, Sanata Kashim Shettima da aka yi a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, ya sanar da Shettima a matsayin abokin takararsa a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli, duk da adawa da aka dunga nunawa kan tikitin Musulmi da Musulmi.
Sai dai kuma a wani yanayi da ke nuna goyon bayan takarar Shettima, kungiyar CAN reshen Borno karkashin jagorancin shugabanta ta yi maraba da wannan zabi na Tinubu, jaridar Punch ta rahoto.
Asali: Legit.ng