Kwankwaso ga Tinubu: Ka bi a hankali, ka kula da lafiyarka, ka bar mu da kamfen
- Dan takarar jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso ya bayyana Bola Tinubu a matsayin mutumin kirki kuma mai dabara, kana ya ba shi shawara
- Tinubu, wanda ke neman gaje Buhari a zaben 2023, Kwankwaso ya bukaci ya sassautawa kansa kuma ya tafi ya kula da lafiyarsa
- Kwankwaso wanda yayi magana akan dan takarar na APC da ya zabi Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa ya ce yana mamakin abin da za su yi da ya wuce na Buhari a yanzu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya shawarci Bola Tinubu, mai rike da tutar jam’iyyar APC da ya tafi ya kula da lafiyarsa.
Da yake magana a yayin wata hira da Reuben Abati na AriseTV a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli, shugaban na NNPP ya ce yakin neman zabe yana da matukar tattare da kalubale kuma Tinubu yana bukatar sassautawa saboda lafiyarsa.
Ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Idan ka ga abokina, Bola, ka gaya masa ya bi hankali, kula da lafiyarsa sosai kuma ka tabbatar… saboda ina kaunarsa sosai, abokina ne.
“Wannan yakin mai tsauri ne sosai, yana da bukatar kokari sosai da dai sauransu. Ina fatan zai bi a sannu domin mu ci gaba da fafutukar tabbatar da kasa daya mai karfi da wadata a Najeriya."
Akwai batutuwa na nuna damuwa game da lafiyar Tinubu tun bayan da ya bayyana aniyarsa ta zama shugaban Najeriya na gaba.
A watan Agustan 2021, an yi rade-radin cewa dan takarar na shugaban kasa a jam'iyyar APC na cikin wani mawuyacin hali na rashin lafiya. Daga baya gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ya musanta hakan inda ya ce Tinubu na da lafiya kuma yana da karfi.
Batutuwa game da lafiyar dan takarar na jam’iyyar APC, bai hana shi zagayawa a fadin kasar nan domin neman shawarin shugabanni a matakai daban-daban ba kan takararsa ta shugaban kasa.
Tinubu da Shettima: CAN ta yi bore da martani mai zafi kan tikitin Muslmi da Musulmi
A wani labarin, kungiyar kiristocin Najeriya CAN ta ki amincewa da zabo tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Da yake magana a wata hira da jaridar Punch a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli, mai magana da yawun CAN, Adebayo Oladeji, ya ce yanke irin wannan shawari a cikin kasa mai cike da rudani irin Najeriya, mataki ne da bai dace ba.
Ya bayyana cewa, kasar na da fasto a matsayin mataimakin shugaban kasar kuma ake kashe malamai da mabiya addinin kirista, to lallai babu tabbacin kiristoci za su samu aminci a mulkin Musulmi da Musulmi.
Asali: Legit.ng