Tabdijam: Bidiyon wayar kamfen din Tinubu ta bar 'yan soshiyal midiya baki bude

Tabdijam: Bidiyon wayar kamfen din Tinubu ta bar 'yan soshiyal midiya baki bude

  • Kamfen dai wani kokari ne na 'yan siyasa wadanda ke neman yin tasiri a zukatan masu kada kuri'u gabanin zabe
  • A kasashenmu na Afrika, musamman Najeriya, kamfen na siyasa kan zo da kyaututtuka ko dai na kudi ko wani abun daban, har ma da abinci
  • Gabanin zabukan 2023, wata kungiyar yakin neman zaben APC ta yanke shawarar sauya dabarunta na kamfe ta hanyar bayar da kyautar wayoyi ga masu kada kuri'u

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Hotunan wata wayar salula da aka kera dauke da hotunan Bola Tinubu da tambarin jam’iyyar APC ta bazu a kafafen sada zumunta, gabanin zaben 2023 mai zuwa.

'Yan Najeriya da dama ne suka yada hotuna da bidiyon wayar a shafin Twitter.

A karkashin allon wayar an rubuta 'Vote Bola Tinubu 2023' yayin da a baya kuwa, ga tambarin APC cike da kala rangadadau.

Kara karanta wannan

Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram din da suka tsere

Tinubu ya matsa ya gaji Buhari, ana ta kamfen da waya
Tabdijam: Wayar salula mai alamar Tinubu ya bar 'yan soshiyal midiya baki bude | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Lokacin da aka kunna wayar, abu na farko da za a yi arba dashi shine hoton Tinubu, sannan sai wasu kalmomi suna cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dimokuradiyya ta dogara ne akan tabbacin cewa akwai yiwuwar abin ban mamaki a cikin talakawa."

Wayar kuma tana amfani ni ne da layukan sim guda biyu.

To, wannan sabon salo na raba wayar salulu a lokutan kamfen sabon lamari ne da ba a cika ganinsa ba a Najeriya.

Martanin 'yan Twitter

@@saad_dyuguda:

"Wannan mutumin yana son ya yi amfani da kudinsa ta kowace hanya don lashe zukatan mutane."

@dola_baba

"Wannan mutumin ya fito ya sayi kujerar shugaban kasa ko ta halin kaka. Babu wata alaka daga gare shi ga mutanen da yake so ya mulka; mutane suna ci gaba da magana ne a madadinsa. Za a maimaita abin da ya faru a 2015. Buhari 2.0."

Kara karanta wannan

Da dumidumi: Kimanin fursunoni 600 sun tsere bayan yan Boko Haram sun farmakin gidan yarin Kuje – FG

@CallMeJossy:

"Babu laifi dai kam. Mai karamin buri zai so ya zabe shi ya dauki wannan."

@divinehills:

"Wa zai yi kira da wannan wayar; Meye yasa ba su raba android ba? Wannan karni na 21 ne fa don Allah."

@Biafranboyz:

"Za mu karbi wayar, kuma ba za mu zabe shi ba."

@shekariben:

"Tabdijam, haka abin zai tafi."

Tonon sililin PDP: Akwai babbar magana a 2023, APC ta shirya siyan kuri'u a zabe

A wani labarin, jaridar Leadership ta ruwaito cewa, jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa jam’iyyar APC mai mulki na shirin siyan kuri’u domin lashe zaben shugaban kasa a zaben 2023 da za a yi nan gaba kadan. Shugaban riko na PDP Amb.

Umar Damagun, wanda ya bayyana hakan a jiya, ya bukaci ‘yan Najeriya da su karbi katin zabe na dindindin (PVC), a matsayin wani mataki na kalubalantar tsare-tsaren APC.

“Abin da suke tunani shi ne a 2023, za su zo su saye ku su ci gaba da bautar da ku, su bar ku a gida, su rufe makarantunku, su ba ku damar zama 'yan bindiga. Ya rage naku yanzu ku fita can ku nemi PVC dinku.

Kara karanta wannan

Hukumar yansanda ta karyata zargin kai wa cocin Anambara hari da Fulani suka yi

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.