‘Dan takaran wucin-gadi zai zama ala-ka-kai, an ce kotu ta hana Tinubu canza ‘Dan takara

‘Dan takaran wucin-gadi zai zama ala-ka-kai, an ce kotu ta hana Tinubu canza ‘Dan takara

  • An samu ‘ya ‘yan jam’iyyar APC da suka shigar da karar Bola Tinubu mai takarar shugaban kasa
  • ‘Yan jam’iyyar sun dumfari kotu da nufin hana ‘Dan takarar canza sunan Kabiru Ibrahim Masari
  • Lauyoyi su na ganin doka ba ta halattawa Tinubu sauya Masari da sunan wani abokin takara ba

Abuja - Wasu mutane biyu da jagorori ne a jam’iyyar APC mai mulki sun je gaban kotu domin a hana APC canza sunan Alhaji Kabiru Ibrahim Masari.

Jaridar Daily Trust ta ce wadannan jiga-jigan jam’iyya su na so babban kotun tarayya da ke zama a Abuja ta hana Bola Tinubu damar canza abokin takara.

‘Ya ‘yan jam’iyyar mai mulki; Zakari Maigari da Zubainatu Mohammed sun shigar da kara mai lamba FHC/ABJ CS/1059/2022 ne a ranar Litinin dinnan.

Lauyoyin Zakari Maigari da Zubainatu Mohammed sun fadawa kotun na garin Abuja cewa cire sunan Kabiru Masari yana nufin an bata tikitin takarar APC.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Dan takarar mataimakin gwamnan APC ya tsallake rijiya da baya a wani farmaki

The Guardian ta ce wadanda suka shigar da karar su na tunanin sassa na 142(1); 29(1), 31 da na 33 na dokar zabe ba zu su bari a taba sunan ‘dan takara ba.

Lauyoyin wadannan mutane biyu sun ce Bola Tinubu da Kabiru Masari su na neman takara ne tare, saboda haka ba za a iya cire sunan wani daga cikinsu ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tinubu
‘Dan takaran APC Bola Tinubu Hoto: @APCOfficialNg
Asali: UGC

Sai yadda Alkalai su ka ce

Alkalai za su yi fashin bakin abin da dokar kasa ta ce domin jin ko zai yiwu a sauya sunan Kabiru Masari daga matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Idan an cire sunan Masari, za a maye gurbinsa da sunan wani dabam a jam’iyyar APC. Lauyoyi su na ganin dokar zabe na kasa ba ta bada damar ayi hakan ba.

Shi dai ‘dan takaran na jam’iyyar APC ya kai wa INEC sunan Masari ne a matsayin wucin-gadi da nufin zai gabatar da asalin Abokin takararsa a watan Yuli.

Kara karanta wannan

Za a jikawa Jam’iyyar APC aiki, an maka IGP a kotu kan binciken Tinubu da aka yi a 1999

‘Dan takaran na APC yana fama da shari’a dabam-dabam a kotu. A baya wasu sun kai karar shi a kan zargin yi wa hukumar INEC karya a game da takardunsa.

Rahoton ya ce har zuwa yanzu ba a sa ranar da Alkali zai saurari karar domin yin hukunci ba.

'Dan takara ya shirga karya

Bayan dawowar Peter Obi daga Masar, sai aka ji labari ya fito yana fadawa mutane cewa kwangilar Siemens da aka bada a Najeriya ba ta je ko ina ba har yanzu.

Mun samu rahoto Mai taimakawa shugaban Najeriya, Tolu Ogunlesi ya yi wa ‘dan takaran raddi da cewa an yi nisa a aikin da zai inganta lantarki

Asali: Legit.ng

Online view pixel