Jerin mutum 11: Buhari ya yiwa majalisar ministocinsa garambawul
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa majalisar ministocinsa garambawul bayan amincewa da wadanda ya nada
- Shugaban ya kuma rantsar da mutum bakwai da ya zaba domin maye gurbin ministocinsa da suka yi murabus
- A baya dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi takardun ajiye aiki na wasu ministocinsa da suka nufi tsayawa takara a zaben 2023
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul da sabbin ministoci da aka ba shi mukamai.
TheCable ta fahimci cewa mukaman ministoci 11 ne hakan ya shafa a wannan sabon garambawul da ya zo gabanin babban zaben 2023.
Ga jerin garambawul din Buhari:
- Adeleke Mamora - ministan kimiyya da fasaha (tsohon karamin ministan lafiya)
- Mu’azu Jaji Sambo - ministan sufuri (tsohon ministan wutar lantarki)
- Umanna Okon Umanna - ministan harkokin Neja Delta
- Sharon Ikeazor - karamin ministan Neja Delta (tsohon karamin ministan muhalli)
- Gbemisola Saraki - karamar ministar ma’adinai da karafa (tsohuwar karamin ministan sufuri)
- Umar Ibrahim EI-Yakub - minista, ayyuka da gidaje
- Goodluck Nanah Opiah - karamin ministan ilimi
- Ekumankama Joseph Nkama - karamin ministan lafiya
- Ikoh Henry Ikechukwu - karamin ministan kimiyya da fasaha
- Odum Udi - karamin ministan muhalli
- Ademola Adewole Adegoroye - karamin ministan sufuri
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hakazalika ministoci bakwai da majalisar dattawa ta tabbatar da nadin su a ranar 29 ga watan Yuni shugaban kasa ya rantsar da su a gaban taron majalisar zartarwa ta tarayya, kamar yadda PM News ta ruwaito.
Ministocin sun hada da: Umanna, El-Yakub, Opiah, Nkama, Udi, Adegoroye da kuma Ikechukwu.
An nada su ne domin cike gurbin da Rotimi Amaechi, Ogbonnaya Onu da wasu biyar da suka yi murabus a watan Mayu domin cimma burin siyasa.
Nadin sabbin ministoci: Na so Buhari ya dawo da Amaechi bisa dililai, Shehu Sani
A wani labarin, tsohon sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce ya so ace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake zabar Rotimi Amaechi a matsayin ministan sufuri.
Daily Trust ta rahoto cewa Sani ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 21 ga watan Yuni, a yayin hira da gidan talbijin na Channels.
Buhari dai ya aika da sunayen mutane bakwai zuwa majalisar dattawa domin a maye gurbinsu da ministocin da suka yi murabus don neman mukaman siyasa.
Asali: Legit.ng