Okupe: Abin da ya sa tun tuni Peter Obi ya yi watsi da maganar dunkulewa da Kwankwaso

Okupe: Abin da ya sa tun tuni Peter Obi ya yi watsi da maganar dunkulewa da Kwankwaso

  • Doyin Okupe ya bayyana abin da ya sa Peter Obi ba zai karbi takarar mataimakin shugaban kasa ba
  • ‘Dan siyasar ya tabbatar da cewa hadewar LP-NNPP ta wargaje tun kwanaki saboda wasu dalilai
  • Okupe yana ganin ba maganar dadewa a siyasa ake yi ba, Obi ne ya san yadda za a gyara Najeriya

Abuja - Dr. Doyin Okupe ya tattauna da gidan talabijin na Channels TV a ranar Talata, 5 ga watan Yuli 2022, inda ya tabbatar da cewa LP ba za ta hade da NNPP ba.

Na hannun-daman na Peter Obi ya bayyana cewa tun makonni hudu da suka wuce maganar hadewar jam’iyyarsu ta LP da ‘yan bangaren NNPP ta tsaya cak.

An ji Okupe yana cewa shi ya jagoranci batun dunkulewar, kuma LP ta yi watsi da batun. A cewarsa, abin ya faskara ne saboda rikicin wanda za a ba tikiti.

Kara karanta wannan

Ana tsoron ‘Yan bindiga sun aukawa gidan yarin Kuje, inda DCP Abba Kyari su ke daure

Legit.ng Hausa ta bibiyi wannan tattaunawa, inda Dr. Okupe ya ce yunkurin hada-kan ya zo karshe ne a lokacin da aka tabo maganar yankin da za a ba takara.

Lokacin mulkin Kudu ne - Okupe

Tsohon hadimin shugaban kasar ya ce babu adalci idan aka ba mutumin Kano takarar shugaban kasa a lokacin da Muhammadu Buhari daga Katsina zai bar ofis.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma ‘yan bangaren jam’iyyar NNPP su na ganin hakan ba laifi ba ne, daga nan batun ya wargaje.

Peter Obi a Bayelsa
Peter Obi mai neman mulki a LP Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Kwankwaso: Ba a nan ta ke ba inji LP

Kamar yadda The Cable ta fitar da rahoto, Okupe ya yi watsi da hujjojin da ‘Yan NNPP suke kawo na cancantar Peter Obi ya zama mataimakin Rabiu Kwankwaso.

“Kwankwaso ya zo gidan talabijin yana nuna kabilanci, yana cewa Arewa ba za su zabi ‘dan takara daga Kudu maso gabas ba.”

Kara karanta wannan

2023: Idan Har Ka Ajiye Okowa, Ba Zaka Samu Kuri'an Igbo Ba, Matasan Ohanaeze Sun Gargadi Atiku Da PDP

“Wannan mutumi ne da ya tsuke kan shi a iyaka jihar Kano, wannan ita ce matsalar, yana yi wa komai kallon Kwankwsiyya.”
“Ya za ayi maganar girma a siyasa? Ana maganar shekara ko dadewa a siyasa ne? Batun wanda zai iya magance matsalar ake yi.”

Tun tuni aka yi watsi da maganar hada-kai, Okupe ya ce sun yi shiru ne kurum saboda dattaku. Nan da Juma’a ake sa ran jin wa Peter Obi zai dauka takara.

Premium Times ta ce daga cikin wadanda ake la’akari akwai Sanata Yusuf Datti Baba Ahmed.

LP ta yi zama da Zakzaky

Mu na da labari cewa ‘Dan takarar Jam’iyyar LP na kujerar Gwamna a jihar Kaduna, Shunom Adinga ya ce sun zauna da Islamic Movement in Nigeria.

Shunom Adinga ya nemi shugaban kungiyar IMN, watau Ibrahim Zakzaky ya marawa jam'iyyar hamayya ta LP baya a matakin jiha da kasa a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Bai Zagi Kudu Maso Gabas Ba, Ba A Fahimce Shi Bane, Shugaban NNPP

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng