Ana tsoron ‘Yan bindiga sun aukawa gidan yarin Kuje, inda DCP Abba Kyari su ke daure

Ana tsoron ‘Yan bindiga sun aukawa gidan yarin Kuje, inda DCP Abba Kyari su ke daure

  • Ana zargin ‘yan bindiga sun nemi su aukawa babban gidan gyaran halin nan na Kuje a garin Abuja
  • Mutane sun ji karar wani abin da ake tunani bam ne, daga nan kuma sai ga harbe-harben bindigogi
  • Har zuwa yanzu, jami’an tsaro da Hukumar gidan yari ba su kai ga magana kan abin da ya faru ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - A yammacin Talata, 5 ga watan Yuli 2022, wasu mutane da ba a san su wanene ba, sun kai hari a babban gidan gyaran hali na Kuje a garin Abuja.

Rahoton da Punch ta fitar ba da dadewa ba, ya tabbatar da cewa wasu mazauna Kuje sun ji karar fashewar wani abin mai kama da bam a yankin Shetuko.

Zuwa lokacin da aka tattara rahoton, jaridar ta ce ba ta iya gano abin da ya jawo wannan harin ba. Ana zargin cewa ‘yan bindiga ne suka kawo hari a yankin.

Kara karanta wannan

Wanda aka yi a idonsa, ya bada labarin yadda Miyagu suka aukawa Ayarin Shugaban kasa

Babban jami’in rundunar ‘yan sanda na garin Abuja, AIG Aliyu Ndatsu ya shaidawa manema labarai cewa sun samu labarin, kuma za su fitar da jawabi.

The Cable ta yi kokarin tuntubar kakakin ‘yan sanda ta Abuja, Josephine Adeh, amma ba a dace ba.

Za a kutsa gidan maza?

Wani mazaunin unguwar ya fadawa manema labarai cewa sun ga wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne su na yawo a wajen wata makaranta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gidan yarin Kuje
Wani gidan yari a Najeriya Hoto: premiumtimesng.com/VenturesAfrica
Asali: UGC

Ba a san inda wadannan mutane da aka gani a wajen makarantar sakandaren gwamnati suka nufa ba, sai kuma aka rika jin harbe-harbe na fiye da minti 30.

“Ba mu san su wanene ba. Mun ji kara kabar fadin wani karfe, kafin mu iya cewa wani abu, sai ga mutane su na ta kai koma a cikin makarantar da ba kowa.”

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun jikkata yayin da yan daba suka farmaki taron PDP a Kogi

- Mazaunin yankin

Rahoton This Day ya ce an ji karar tashin wani abu mai kama da bam ne bayan karfe 10:00 na dare, daga nan kuma sai karan bindigogi suka biyo baya.

Har yanzu jami’an gidan gyaran halin ba su yi wa al’umma karin haske ba. Amma dai an tabbatar da cewa abin ya lafa, daga baya an daina jin harbe-karben.

Wani rahoton ya ce sai da hukuma ta sanar da cewa akwai masu shirin kawowa gidan yarin hari.

Abba Kyari su na tsare

Rade-radin da ke yawo shi ne wasu miyagun ‘yan bindiga sun yi kokarin aukawa gidan yari na Kuje. A baya an yi yunkurin fasa gidan gyaran hali a Najeriya.

A wannan gidan gyaran hali ne babban jami’in ‘yan sanda DCP Abba Kyari da wasu suke tsare. Kwanakin baya ya koka da cewa rayuwarsa ta na cikin hadari.

Kun samu labari cewa kimanin mutane 190 ne a gidan gyaran halin na Kuje suka yi yunkurin hallaka Abba Kyari saboda sun dade su na rike da shi a zuciya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel