Gabanin 2023: ‘Yan kasuwan Sokoto sun bar APC sun kama PDP bisa saba alkawuran APC
- Jam'iyyar PDP ta yi babban kamu a jihar Sokoto, yayin da 'yan kasuwa matasa suka yi waje da akidar APC
- Da suke komawa jam'iyyar PDP mai mulkin jihar, sun kuma bayyana cewa sun ji kunya yadda gwamnatin APC ta sauya alkawuranta
- A baya gwamnatin APC ta Buhari ta yi alkawarin tallafawa wasu 'yan kasuwa a Sokoto da iftila'in gobara ya rutsa dasu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Sokoto - 'Yan kasuwa a Sokoto sun fice daga APC zuwa PDP saboda rashin cika alkawura da APC ta yi wa Kungiyar matasan ‘yan kasuwan jihar Sokoto.
Sun koma PDP, jam'iyya mai mulki a jihar domin marawa tafiyar jam'iyyar baya a zabuka da ke tafe a 2023.
Rahoton Daily Trust ya ce, ’yan kasuwar da suka yi tir da kasancewarsu a jam’iyyar APC sun yi ficewarsu daga cikinta ne a cibiyar tarihi da ke Sokoto.
Babu ruwanmu da kai namu ne: Jiga-jigan APC a mahaifar Atiku sun sha alwashin ganin bayansa a zaben 2023
Sun kuma yi Allah wadai da saba alkawarin ba da tallafi ga wadanda gobarar da ta tarwatsa sassan babbar kasuwar Sokoto a farkon shekarar da ta gabata da tawagar gwamnatin tarayya ta yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daya daga cikin jagororinsu Shuaibu Yellow ya bayyana cewa:
“Wannan alkawarin da bai cika ba na daya daga cikin manyan dalilan da suka sa muka fice daga jam’iyyar."
Jaridar Punch ta ruwaito wani ma Alhaji Abubakar Kalambaina ya bayyana cewa:
“A matsayinmu na matasa mun yanke shawarar tsara wa kanmu sabuwar hanya ne saboda shugabancin da muke da shi a yanzu ya ci amanar da muka ba shi.
“Sun yi watsi da jindadin mu don son kansu. Suna zuwa wurin shugabannin tsohuwar jam’iyyarmu su dawo mana da labarin kanzon kurege yayin da wasu mambobinmu ke kage.”
2023: 'Yan Najeriya sun kagu a fatattaki APC a kasa, inji dan takarar NNPP Kwankwaso
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Alhaji Rabi’u Kwankwaso, ya ce daga dukkan alamu ‘yan Najeriya sun gaji da jam’iyyar APC mai mulki, kuma suna da burin ganin karshen gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Kwankwaso ya yabawa dimbin jama’a da suka fito domin tarbarsa a jihar Gombe da yammacin ranar Asabar, inda ya bayyana hakan a matsayin wata alama da ke nuna cewa jama’a a shirye suke don samun damar kawar da gwamnatin APC a zaben 2023.
Kwankwaso, wanda ya je Gombe domin kaddamar da ofishin jam’iyyar, ya ce dimbin jama’a da suka fito domin tarbarsa daga filin jirgin sama zuwa cikin garin, sun zaburar da shi cewa jihar Gombe ta shiga sahun su Kano wajen jihohin Kwankwasiyya.
Asali: Legit.ng