Magoya bayan PDP a jihar Borno sun fatattaki shugaban jam’iyyar, sun hana shi shiga sakatariyarta

Magoya bayan PDP a jihar Borno sun fatattaki shugaban jam’iyyar, sun hana shi shiga sakatariyarta

  • Daruruwan fusatattun matasan PDP sun fatattaki dakataccen shugaban jam’iyyar a jihar Borno, Hon Zanna Gadama a ranar Lahadi, 3 ga watan Yuli
  • Matasan sun hana Gadama shiga sakatariyar jam’iyyar da ke Maiduguri bayan ya kira wani taro na masu ruwa da tsaki da manema labarai
  • Suna dai zargin dakataccen shugaban da wawure kudaden jam’iyyar da kuma yi mata zagon kasa don kada ta kai labari a zabe

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Borno - Fusatattun mambobin PDP a ranar Lahadi, sun mamaye sakatariyar jam’iyyar da ke Maiduguri don hana dakataccen shugaban jam’iyyar reshen jihar Borno, Alhaji Zanna Gadama, shiga ofishinsa don gudanar da wani taro da jawabi ga manema labarai.

Gadama ya gayyaci manema labarai don su nadi taron masu ruwa da tsaki da ya kira bayan dakatar da shi da wasu jami’an jam’iyyar suka yi kwanaki da suka wuce, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Najeriya sun gaji da APC, Kwankwaso ya ce ya hango karshen APC

Mambobin PDP
Magoya bayan PDP a jihar Borno sun fatattaki shugaban jam’iyyar, sun hana shi shiga sakatariyarta Hoto: Daily post
Asali: UGC

Sai dai kuma, da shigarsa sakatariyar ya tarar da magoya bayan jam’iyyar wadanda suka mamaye dakin taron inda suka bukaci ya fice daga harabar wajen.

Magoya bayan jam’iyyar wadanda suka yi tofin Allah tsine ga dakataccen shugaban sun zarge shi da wawure kudaden jam’iyyar tsakanin 2019 zuwa yau, jaridar Leadership ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sun kuma sha alwashin cewa idan ba a tsige shi a matsayin shugaban jam’iyyar PDP a Borno ba daga jam’iyyar har dan takararta shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ba za su samu kuri’unsu ba.

Hakazalika, sun zargi shugaban jam’iyyar da hada kai da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar don kifar da jam’iyyar a duk shekarun zabe.

PDP ta dakatar da shugabanta a wata jihar arewa, ta bayyana dalili mai karfi

Kara karanta wannan

Kafin 2023: Tashin hankali a APCn Katsina, dubban mambobi sun fece zuwa PDP

A baya mun kawo cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Borno a ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni, ta dakatar da shugabanta, Alhaji Zannah Gadama, kan cin dunduniyar jam’iyyar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da aka fitar a karshen wani taron gaggawa da aka kira dauke da sa hannun bai ba PDP reshen jihar shawara kan doka, Mista Abdu Jidda a Maiduguri a ranar Alhamis, jaridar The Nation ta rahoto.

Ya ce an samu shugaban jam’iyyar da hannu wajen yiwa jam’iyyar makarkashiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng