Tsaka mai wuya: Dubban mambobin APC sun sauya sheka zuwa PDP a wata jahar arewa

Tsaka mai wuya: Dubban mambobin APC sun sauya sheka zuwa PDP a wata jahar arewa

  • Guguwar sauya sheka ta kado inda dubban yan kasuwa a Sokoto suka fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP mai mulki a jihar
  • Masu sauya shekar sun zargi shugabannin tsohuwar jam’iyyarsu da yin watsi da su da kuma rashin kula da jin dadinsu

Sun kuma zargi gwamnatin tarayya da kin cika alkawaran da ta daukar masu a lokacin da gobara ta lakume shagunansu a babbar kasuwar Sokoto a farkon shekarar nan

Sokoto - Dubban mambobin kungiyar matasan ‘yan kasuwa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Sokoto sun sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Hakan na zuwa ne bayan sauya sheka da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar suka yi zuwa PDP mai mulki a jihar a kwanaki.

Yan kasuwar wadanda suka yi watsi da kasancewa yan APC a cibiyar tarihi ta jihar Sokoto sun bayyana kyakkyawar shugabanci da budaddiyar manufar Gwamna Aminu Tambuwal ga dukkanin al’ummar jihar a matsayin hujjarsu, jaridar Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Najeriya sun gaji da APC, Kwankwaso ya ce ya hango karshen APC

PDP da APC
Tsaka mai wuya: Dubban mambobin APC sun sauya sheka zuwa PDP a wata jahar arewa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun kuma bayyana son kai da watsi da jin dadinsu da tsoffin shugabanninsu suka yi a matsayin dalilinsu na sauya sheka, jaridar Punch ta rahoto.

Daya daga cikin wadanda suka yi tsokaci a taron, Shuaibu Yellow, ya yi zargin cewa har yanzu ba a cika alkawarin da tawagar gwamnatin tarayya da suka ziyarci jihar lokacin da gobara ta lakume wani bangare na kasuwar Sokoto suka daukar masu ba a farkon shekarar nan.

Yellow ya ce:

“Rashin cika wannan alkawari na daya daga cikin manyan dalilan da suka sanya mu barin jam’iyyar. Dukkaninmu da muka taru a nan yan kasuwa ne kuma tun bayan gobarar, rayuwa ta yiwa yawancinmu wahala.
“Baya ga wasunmu da suka cika shagunansu da kayayyakin da aka bamu a kan bashi sannan har yanzu muke gwagwarmayar biyan bashin, wasun mu na rayuwa ne hannu baka kwarya.”

Kara karanta wannan

Kafin 2023: Tashin hankali a APCn Katsina, dubban mambobi sun fece zuwa PDP

Hakazalika, Abubakar Kalambaina ya ce:

“A matsayinmu na matasa, mun yanke shawarar samawa kanmu sabuwar inuwa saboda shugabancin da muke da su, sun ci amanar yardar da muka basu.
“Sun yi watsi da jin dadinmu don saboda son zuciyarsu. Su kan je ga shugabannin tsohuwar jam’iyyarmu sannan su dawo mana da labarai yayin da wasu daga cikin mambobinmu suka rasa tudun dafawa.”

'Dan majalisa da dubbannin mambobin jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC a jiha ɗaya

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ibarapa Central/Ibarapa a majalisar tarayya, Muraina Ajibola, ya jagoranci dubbannin mambobin jam'iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa APC a jihar Oyo.

Daily Trust ta ruwaito cewa masu sauya sheƙan sun sami kyakkyawan tarba daga shugaban APC reshen jihar Oyo, Isaac Omodewu, ɗan takarar sanatan Oyo ta kudu, Akogun Sarafadeen Alli, da wasu jagororin jam'iyya a ƙarshen makon nan.

Kara karanta wannan

Jirgin Kasan Abj-Kd: Iyalan Fasinjoji Sun Koka Kan Labarin Harbin 1 Daga Cikin Wadanda aka Sace

Honorabul Ajinbola ya bayyana cewa a iya bayanan da ya tattara aƙalla mutum 18,000 ne suka biyo shi zuwa sabuwar jam'iyyarsa APC daga PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng