Hutu dole: Wani hoto ya nuna Atiku da jiga-jigan PDP a Spain suna cin duniyarsu da tsinke

Hutu dole: Wani hoto ya nuna Atiku da jiga-jigan PDP a Spain suna cin duniyarsu da tsinke

  • 'Yan siyasar Najeriya na daukar hutun da ya dace bayan dambarwar siyasar jam'iyyun na cikin gida da zabukan fidda gwani
  • Atiku Abubakar wanda ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na PDP a yanzu haka yana can a birnin Malaga na kasar Spain inda yake rage zafi gabanin zaben 2023
  • A cikin hoton da ya yadu a shafin Instagram, an ga lokacin da Atiku ke tare da wasu jiga-jigai na siyasar kasar nan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Malaga, Spain- An gano hoton dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar a birnin Malaga na kasar Spain yana cin duniyarsa da tsinke.

An ga hoton tsohon mataimakin shugaban kasar ne tare da shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Hon. Ndudi Elumelu.

Elumelu mai wakiltar Aniocha North/Aniocha South/ Oshimili North and South a matsabar tarayya a jihar Delta ya yada hoton a shafinsa na Instagram.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnonin APC sun zauna, sun yi shawarwari kan yankin da zai kawo abokin tafiyar Tinubu

Atiku ya tafi hutun rabin lokaci a kasar Spain
2023: Kwatsam, aka ga dan takarar shugaban kasa na PDP da wasu jiga-jigai a Spain | Hoto: ngelumelu15
Asali: Instagram

Haka nan tsohon mataimakin sakataren yada labaran jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Timi Frank yana tare da jiga-jigan biyu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Atiku wanda ke sanye da karamar rigar Polo mai launin shudi yana cin karin kumallo ne da jiga-jigan na jam'iyyar PDP a birnin Spain.

Atiku ya bar kasar ne kwanaki kadan bayan kammala zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar da ya lashe.

Kujerar Shugaban PDP na lilo bayan sabon rikicin da ya barke kan abokin takaran Atiku

Rigimar da ta barke a jam’iyyar PDP bayan zaman Gwamna Ifeanyi Okowa ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa na 2023 na kara rincabewa.

Rahoton da Daily Trust ta fitar a ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni 2022, ya nuna cewa lamarin ya kai ga ana kiran a sauke shugaban PDP, Dr. Iyorchia Ayu.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya magaantu kan sabon rikicin da ya ɓarke a PDP, ya faɗi matakan da suke ɗauka

Masu neman a tunbuke shugaban jam’iyyar adawar na kasa, har sun soma yada jita-jitar an sauke shi. Tuni sakatariyar jam’iyyar PDP ta karyata labarin nan.

Hadimin shugaban jam’iyyar na PDP, Simon Imobo-Tswam ya ce Iyorchia Ayu bai sauka daga kujerarsa, har Amb. Umar Damagum ya karbi matsayin ba.

Shugaba Buhari ya dira birnin Lisbon, kasar Portugal

A wani labarin na daban, Shugaba Muhammadu Buhari dira Lisbon, babb birbirnin kasar Portugal lafiya a ranar Talata, 28 ga Yunu, 2022.

Buhari Sallau, hadimin shugaban kasan ya bayyana hakan a gajeren jawabi da hotunan da ya fitsr a shafinsa na Facebook.

Yace: ”Shugaba Muhammadu Buhari ya isa Lisbon, Portugal don ziyara tare da halartar taron teku na majalisar dinkin duniya.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel